Abubakar Abba" />

Muna Kan Tattaunawa Da CBN Don Kare Hare-Haren Makiyaya – Fasto Adewumi

Farfado Da Tattalin Arziki

Shugaban manoman Rogo ta kasa (NCGA), Fasto Segun Adewumi ya bayyana cewa, sakamakon tsoron kai hare-haren Fulani Mikiya kan wasu manoma, musamman manoman na Rogo, a yanzu haka, kungiyar bna kokarin samar da jami’an ‘yan sanda da za su dinga yiwa manoman na Rogo rakiya zuwa goanakasnu domin gudanar da aiki.

A cewar Shugaban manoman Rogo ta kasa Fasto Segun Adewumi, lamarin na kai hare-haren Fulani Makiya kan manoman na Rogo ya na kara ta’azzara, inda hakan ya kuma janyo manoman na Rogo da dama a kasar nan suka yi wasti da gonakansu duk da cewa sun ciwo bashi yin noman Rogo.
Shugaban manoman Rogo ta kasa Fasto Segun Adewumi ya bayyana hakan ne a wata hira da Jaridar Nigerian Tribune, inda Shugaban manoman Rogo ta kasa (NCGA), Fasto Segun Adewumi ya bayyana cewa, ya karbi rahotani da ban da ban daga gun ‘ya’yan kungiyar kan hare-haren da Fulani Makiyayan suke kai wa manoamn na Rago dake a daukacin fadin kasar nan a yayain da suke kan yin noma a gonakansu.
A cewar Shugaban manoman Rogo ta kasa Fasto Segun Adewumi “Mu na fuskantar kalubalen hare-haren Fulani Makiyaya a gonakanmu, inda ya kara da cewa, dabobin da Fulani Makiyayan suke kai wa cikin gonakanmu, suna lalata ma na Rogon da muka shuka”.
Shugaban manoman Rogo ta kasa (NCGA), Fasto Segun Adewumi ya kara da cewa, har ila yau kuma, manoman na Rgo na fusknatar kalubalen yin garkuwa dasu domin neman kudin fansa, inda hakan ya janyo manoman na Rogo, bas a iya zuwa gonakansu domin gudanar da aiki”.
A cewar Shugaban manoman Rogo ta kasa Fasto Segun Adewumi, bashin da manoman na Rogo suka karba domin yin aikin noma ba su samu sukunin yin noman ba domin akasarinsu sun yi watsi da gonakan su saboda yawan kai hare-haren na Fulani Makiyaya.
Shugaban manoman Rogo ta kasa Fasto Segun Adewumi ya ci gaba da cewa, “ Mu na kan tattaunawa da babban Bankin Nijeriya kan ya kara bai wa manoman na Rogo a kasar nan wani sabon bashin domin yin noman Rogo da kuma wasu tallafin kudade domin samar wad a manoman na Rogo tsaro don su dinga zuwa gonakansu sun a yin noma ba tare da wata matsalar ta tsaro ta shafe su ba”.
A cewar Shugaban manoman Rogo ta kasa (NCGA), Fasto Segun Adewumi, “Akasarin manoman na Rogo ba sa iya zuwa gonankansu domin gudanar da aiki saboda tsaron ka da masu sace mutane su yi awon gaba da su”.
Shugaban manoman Rogo ta kasa Fasto Segun Adewumi ya kara da cewa, “ Hatta mu kanmu shugabanni sai mun yi hayar ‘yan sanda da za su yi ma na rakiya zuwa gonakanmu sannan mu ke iya zuwa gudanar da aiki a gonakanmu”.
A cewar Shugaban manoman Rogo ta kasa Fasto Segun Adewumi, kasashen duniya da suka ci gaba, ana samar wa da manoman dake a kasar wuraen yin noma ba tare da wasu dabbobi sun yi masu kuste a gonakansu ba.
Shugaban manoman Rogo ta kasa (NCGA), Fasto Segun Adewumi ya kara da cewa, “ Mun ga yadda ake yi a wasu kasashen duniya da suka ci gaba, musamman kan fannin noman Rogo, inda ya yi nuni da cewa, fannin na bayar da gagarumar gudunmawa wajen kara bunkasa tattalin arzikin kasashen da kuma kara samar masu da dimbin kudaden shiga masu yawa”.
A cewar Shugaban manoman Rogo ta kasa Fasto Segun Adewumi, a yaznu haka ana fitar da Rogo zuwa kasuwannin duniya da ya kai kashi 90 a cikin dari.
Shugaban manoman Rogo ta kasa (NCGA), Fasto Segun Adewumi ya kara da cewa, a irin wadannan kasashen, babu inda ake yin kiwo a fili kamar yadda ake yi a kasar, inda ya ce, ya na da yakinin gwamnatin za ta dauki matakan da suka dace, domin kare manoman na Rogo daga hare-haren na Fulani Makiyaya a kasar nan a yayain da suke kan yin nomansu a gonakansu.

Exit mobile version