Sharfaddeen Sidi Umar" />

Muna Kashe Milyoyin Kudade Domin Yaki Da Ta’addanci A Sakkwato –Tambuwal

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta na kashe miliyoyin kudade a kowane wata domin kare afkuwar ayyukan ta’addanci a kokarin tabbatar da tsaron rayukan al’umma da dukiyoyin su.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ya bayyana hakan a yayin kaddamar da Gadar takawa da kafafu a Kofar Mata mai tsawon mita 120 a Jami’ar Usmanu Danfodiyo wadda Bankin UBA ya gina a karkashin Gidauniyar UBA domin amfanin daliban jami’ar.

Gwamna Tambuwal wanda ya bayyana muhimmancin saka jari a fannin ilimi, ya nuna damuwar yadda yaki da ‘yan ta’adda ke canyewa Jigar Sakkwato makuddan kudade.

“Muna kashe miliyoyin kudade a kowane wata a sha’anin tsaro musamman a bisa ga matsalolin tsaro da ke faruwa a Zamfara. Jami’an tsaron mu suna zaune a cikin shirin ko-ta-kwana domin ganin ba mu fuskanci abin da ke faruwa a Jihar Zamfara ba.” In ji Gwamnan.

Tambuwal wanda Sakataren Gwamnati, Farfesa Bashir Garba ya wakilta ya kuma yi kira ga cibiyoyin kasuwanci masu zaman kansu da su rika taimakawa wajen bunkasa sha’anin ilimi da tsaro a kasar nan.

Da yake kaddamar da gadar, Gwamna Tambuwal ya yabawa Bankin UBA kan kokarin da suka yi na gina gadar wadda ya bayyana cewar za ta saukakawa dalibai zirga-zirgar su tare da fatar sauran cibiyoyin kasuwanci za su yi koyi da Bankin UBA.

A jawabinsa Shugaban Rukunin Bankin UBA, Mista Kennedy Uzoka ya bayyana cewar gina gadar yana daya daga cikin hobbasar bankin na tallafawa al’umma a fannonni daban-daban.

“Bankin UBA ya ga wajibcin gina wannan gadar domin saukakawa dalibai wahalhalun da suke fuskanta a jami’ar. Gina wannan gadar da muka yi a yanzu dalibai za su rika wucewa ba tare da wata tangarda ba, ba kuma tare da sun yi tafiya mai nisa ba domin zuwa dakunan kwanansu. Wannan gadar ta takaita lokaci, kuma za ta baiwa dalibai damar karatu sosai. Mun gina dakunan kwanan dalibai a yanzu kuma ga gada mun gina.”

A  jawabinsa, Shugaban Jami’ar Danfodiyo, Farfesa A.A Zuru ya bayyana cewar daliban jami’ar sun shafe tsayin shekaru da dama suna shan bakar kwakwa a dalilin rashin gadar wadda ya ce ginata ba karamin taimako ba ne ga jami’ar da daliban ta don haka ya jinjinawa Gidauniyar UBA kan namijin kokarin da suka yi na inganta sha’anin karatu da kyautata jin dadin dalibai.

 

Exit mobile version