Muna Kiyaye Wa Wurin Ɗaukar Ma’aikata -Kwamanda Joshua

BALA JOSHUA shi ne Kwamanda na rundunar farin kaya na Peace Corp a Jihar Nasarawa. Ya ƙaryata jita-jitar da ake yaɗ a wa cewa suna karɓan kuɗ i wajen jama’a. A tattaunawarsa da wakilin LEADERSHIP A Yau ZUBAIRU T.M.LAWAL  yayi cikakken bayani. Ga yadda hirar ta kasance:

Game da ɗ ibar ma’aikata na tsaro a hukumar farin kaya na Peace corp wane shirye-shirye kuke ciki a nan Nasarawa?

Ka san cewa mun yanzu hukumar Peace Corp muna nan tamkar NGO ne saboda Gwamnati har yanzu ba ta rattaba hannu a kan batun Peace corp ba tukuna. Amma yanayin da muke yanzu duk wanda ya nuna sha’awarsa ga aikin yakan sayi Takardar Neman Shiga sai ya cika sai a tantance mutu sannan a fara horar da su ka ji.

Ya zuwa yanzu a  nan Jihar Nasarawa mutum nawa kuka ɗ iba kuke aiki da su?

Gaskiya a nan Jihar Nasarawa muna da matasa kusan dubu uku kuma waɗ anda kake ganin su yanzu tun na waccan shekarar ne da muka ɗ iba waɗ anda ba a tantance su ba, aka samu matsala da rundunar ’yan sanda. Shi ne ka dakata yanzu kuma suka zo ake tantance su kafin a horar da su a ba su kayan Peace Corp su cigaba da gudanar da aikin samar da zaman lafiya a ƙasa.

A kwanakin baya Majalisar Dattijai ta ƙasa ta bayyana ƙudurinta na amincewa da wannan rundunar kiyaye zaman lafiya na Peace Corp, inda ta rattaba hannu a kan takardar amincewa sannan ta miƙa ta ga fadar Gwamnatin Tarayya inda ake jiran Shugaban ƙasa ya sanya hnnu.

Yaya kuka ji da wannan albishirin?

Abin farin ciki ne abu ne da muka daɗ de muna adu’a Allah ya kawo mana wannan ranar sai ga shi majalisar Dattijai ta ƙasa ta sanya hannu yanzu ana jiran fadar Shugaban ƙasa ne ya sanya hannu ai dole mu yi murna. Sama da shekara sha tara muna aiki kuma Gwamnati tana ganin abin da muke yi ka ga ai ta yaba ke nan da abin da muke yi.

Akwai rundunar ’Yan sanda da na Ciɓil difence (SCDEC) waɗ anda ayyukansu shi ne samar da tsaro, shin ku a naku ɓangaren wane irin aiki za ku samar a ƙasa?

Aikin ɗ an sanda shi ne samar da tsaro ta yadda kowa zai kiyaye doka ya kuma kama mai lefi ya kai a hukunta shi. Su kuma (SCDEC) aikinsu kiyaye kayayyakin gwamnati. Mu kuma aikinmu tallafa wa dukkaninsu. Sannan a yadda Majalisar Dattijai ta sanya mu shi ne kiyaye makarantun Gwamnati ta hanyar ba da kulawa . Saboda ana buƙatar kare makarantun ƙasar nan daga miyagun ayyuka. Abu na biyu ’yan sanda da SCDEC dukkaninsu suna riƙe ne da Bindiga amma mu babu batun riƙe Bindiga a tsarinmu, saboda aikinmu wayar da kai ne a samu zaman lafiya.

Wani lakocin a ɓangaren tsaro akan ɗ auki ɓata gari ya kasance sun kawo lalacewar aiki shin a wajen ɗ aukar ma’aikata kuna kiyayewa da hakan?

Babu shakka ko a haihuwa idan mutum yana da ’ya’ya da yawa ba za a rasa waɗ anda suke da wasu halaye na daban ba. Amma abu mafi mahimmanci a matsayinka na Uba dole ka sanya ido kan ’ya’yanka ka ga waye yake da wata ɗ abi’a ta daban. Kuma ka san matakan da za ka ɗ auka na gyara a kansa. Babu shakka muna da tsarin cewa idan muka samu wani mai mummunar hali wanda kuma halin nasa bai cancanta ya zauna tare da mu ba to za mu sallame shi ya ƙara gaba. Saboda mu ana samar da mu ne domin kulawa da yanayin al’umma da samun zaman lafiya bai kamata a ce a samu ɓatagari cikinmu ba.

Akwai masu cewa sukan biya kuɗ i amma ba su ga sunayensu ba, shin mene ne gaskiyar maganar?

Duk wanda ya ce ya biya kuɗ i sannan aka ɗ auke shi a aiki wallahi ya yi ƙarya. Abin da mutum zai saya shi ne Fam na Naira 1,500 ya je ya cike ya dawo da shi. Kuma za mu gaya maka cewa har yanzu Gwamnati ba ta anshe mu ba, dan haka za ka biya Naira 40,000 na kayan sawa da za a ba ka da takardu sannan wajen horarwa ai ba kyauta ake aikin horarwa ba kai ma za ka sha ruwa a nan. Na samu labarin masu cewa sun kashe kuɗ i kamar 200,000 ko 300,000 kafin ya samu wannan aiki. To na daɗ e ina ƙalubalantar su idan da wanda ya kashe sama da 40,000 to ya zo nan ofishina ya gaya min, zan bincika in ji inda ya kasha waɗ annan kuɗ in na karɓo masa haƙƙinsa. Na san dai akwai wasu ƙungiya waɗ anda sunansu da kakinsu ya so ya zama irin namu amma akwai bambamci kila ko ta nan ne amma mu ba mu karɓar kuɗ i da sunan ba ka matsayi ko wani abu.

Sau da yawa cikin ma’aikata akan samu ɓata gari da ke karɓar kuɗ i wajan mutane da sunan za su samar masu aiki an taɓa samun wannan a gurinku?

Babu shakka an taɓa samu, a kwai wanda ya taɓa karɓan kuɗ in wani da sunan zai samar masa da aiki, muka zo da shi nan muka sanya shi ya mai da masu da kuɗ insu.

Ka san yanayin yadda ƙasarmu ta lalace kowa yana burin ya yi arziki. Kuma wannan ba shi ne yake sawa ka yi arziki ba, duk wanda muka samu da wannan ɗ abi’a mukan hukunta shi.

A halin yanzu wane irin tallafi kuke samu daga Gwamnatin Jihar Nasarawa?

Abin yabawa ne ga gwamnatin Jihar Nasarawa saboda suna ba mu goyon baya mu aiwatar da ayyukanmu ba tare da wata matsala ba. Kuma da zarar Gwamnati tana da abin yi muna fita mu tallafa mata. Kuma lokacin Sallah da sauran bukukuwa Gwamnati na taimaka mana daidai gwargwado. Akwai kyakkyawar dangantaka tsakaninmu da Gwamnatin Nasarawa. Tana ba mu abin da za mu bai wa ma’aikatanmu saboda su ciyar da iyalansu, mu kuma muna iya ƙoƙarinmu mu ga mun taimaka wajen samar da zaman lafiya cikin wannan jihar.

Akwai koken da kuka taɓa kai wa Gwamna Almakura dangane da yanayi?

Gaskiya ba mu taɓa kai masa wani kuka ba, saboda Gwamnatin tarayya ba ta rattaba hannu kan takardar tabbatar da mu ba. Kuma ka ga Gwamna yakan bai wa jami’an tsaro waje na dindindin to waɗ annan Gwamnatin tarayya ta rataba hannu a takardarsu ne. Amma kamar yadda yake da yaƙini da zarar muma an sanya hannu kan takardarmu na san Almakura zai yi mana irin wannan gatar.

Wace fata kuke da shi na samar da zaman lafiya a jihar da ƙasa baki ɗ aya?

Gaskiya fatarmu ita ce kamar yadda yanzu aka samu dauwamemen zaman lafiya a Jihar Nasarawa da taimakon Gwamna Umar Tanko Almakura da kuma yadda Shugaban ƙasa ya daƙile da dama daga cikin ta’addancin ’yan Boko -haram Allah ya ƙara cigaba ya bai wa ƙasarmu lafiya

Kuma ina kira ga jama’a da su goya wa Gwamnati baya su ba da haɗ in kai wajen zaman lafiya.

Wanne kira kake da shi ga jama’arku wajen kamanta kyawawan ɗ abi’u?

Nakan gaya masu duk wanda ka ga ya yi suna to ya kamanta aiki mai kyau. Saboda yin abu mai kyau yakan sa a yaba maka idan ka yi mumuna za a yi Allah wadare da kai. Saboda haka su yi aiki tsakani da Allah.

 

Exit mobile version