Shugaban tafiyar kwankwasiyya, Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa, jam’iyar NNPP na maraba da kowa.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne ajiya Talata yayin zantawarsa da Freedom Rediyo a Abuja, ya ce, Jam’iyyar NNPP na maraba da kowa kuma kofa a bude take ga duk mai sha’awar Shiga.
Sanatan ya yi karin haske ne yayin da a ke jita-jitan cewa tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, da sauran ‘yan jam’iyar APC na shirin sauya sheka zuwa NNPP.
“Ko ‘yan G-7, muna maraba da su domin su ma ba sa jin dadin abubuwan dake faruwa a jihar Kano a shekaru bakwai da su ka wuce.
“In dai mu na son NNPP ta girma ta kuma yadu, to dole a baiwa kowa damar ya shiga jam’iyar,” in ji Kwankwaso.