Bala Kukuru" />

Muna Samun Ayyukan Raya Kasa A Jihar Kaduna

Honarabul Alhaji Ado Umar Bagu Hunkuyi mai bai wa shugaban karamar hukumar Kudan Alhaji sha’aibu Bawa Jaja shawara na musamman a kan harkokin siyasa da ayyuka na musamman, ya bayyana cewar tun daga lokacin da jam iyar A.P.C ta karbi ragamar mulkin gwamnatin jihar Kadunaa karkashin gwamnan Malam Nasiru el-Rufai suna ci gaba da samun ayyukan raya kasa tare da nema wa matasa guraben karatu a duk fadin jihar.

Hoarabul  Ado Bagu Hunkuyi ya yi wannan tsokaci ne a Legas a Unguwar Mile 12 a lokacin da ya jagoranci tawagar shugaban karamar hukumar Kudan  Alhaji Sha’aibu Bawa Jaja  zuwa Legas, domin gudanar da ziyara ta musamman tare da ta’aziyar wadansu al’ummar Hausawa dad a suka rasu.

Honarabul Bagu ya ci gaba da cewa, baya ga ayyukan raya kasa da gwamnati jihar Kaduna ke gudanarwa, kananan hukumomi ma ba a barsu a baya ba,  wajen gudanar da ayyukan raya kasa irin wadannan ayyuka in ji shi ko a karamar hukumarsa ta Kudan shugaban karamar hukumar Alhaji Sha’aibu Bawa Jaja yana ci gaba da gudanar da irin wada nan ayyuka na raya kasa da ci gaban al’umma. A cewarsa kadan daga cikin yankunan da suka samu irin wadannan ayyuka a karama hukumar Kudan sun hada da kauyen Danloto da tasha Rice  suka samu gyaran makarantu garin Kauranwali inda suma suka samu gyaran asibitocinsu da sauran kauyuka makamantan wadannan.

Ya ci gaba da cewar sannan ya zakulo  yaran da suka kammala sakandire a karamar hukuman Kudan ya sama musu aikin yi.

Exit mobile version