Mai koyar da ‘yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, Arsene Wenger, ya ce a yanzu ‘yan wasansa suna samun sabon ilmi da gogewa a gasar Europa da suke bugawa a wannan shekarar.
Mista Wenger ya ce, duk da cewa gasar Europa ba ita ce gasar da ya kamata a ce ƙungiyar tana bugawa ba, amma ‘yan wasansa suna sake samun tunani da ƙwarewa wajen buga wasa a inda basu taɓ a zuwa ba, sannan kuma suna samun sabuwar gogewa a wajen sauyin yanayi da suke samu a ƙasashen da suke zuwa wasa.
Wannan dai shi ne karo na farko da Arsenal ɗin ba ta buga gasar cin kofin zakarun Nahiyar turai ba cikin shekaru 20 wanda kamar yadda wenger ya bayyana sabon ilmi ne.
Wenger ya ce, yana son ƙungiyar ta lashe gasar ta Europa, domin samun tikitin gasar zakarun turai a shekara mai zuwa, duk da cewa ba lashe kofin na Europa kawai ne hanyar zuwa ba, domin idan suka ƙare a cikin ‘yan hudun farko na firimiya za su je wanda daman ita ce hanyar da suka saba zuwa gasar.
A ƙarshe ya ce duk da cewa yanzu an zo lokacin da babu hutu domin bayan wasan Europa akwai wasan firimiya da za su fafata da Eɓ erton a ranar lahadi, sannan sai gasar Ƙarabao a ranar talata.