Bala Kukuru" />

Muna Samun Saukin Cinkoson Motocin Sufiri A Apapa

Daya daga cikin shugabannin masu kula da harkokin manyan motocin sufiri masu dakon kaya daga Legas zuwa Arewacin Nijeriya N.U.R.T.W Alhaji Ummaru Kazaure mai kula da ofishin na 02  shiyar Unguwar mile12 ta jihar Legas, ya bayyana cewa ana ci gaba da samun saukin cinkoson da ke faruwa a Apapa na manyan motocin sufiri masu dakon kaya daga Legas zuwa Arewacin Nijeriya Kazaure ya fadi haka ne a ofishinsa na 02 a unguwar Mile 12 a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida  game da abubuwan da ke ci wa harkokin sufiri na manyan motocin dakon kaya tuwo a kwarya a cikin garin Legas da kewaye.

Ya ci gaba da cewa, a yanzu haka sakamakon wani aiki na hadin gwiwa wandan aka yi  tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Legas wanda shi ya yi sanadiyyar samun saukin cinkoson manyan motoci a unguwar  Apapa a wannan lokaci in ji shi.

Tunda an kwashe kaso sabain a cikin dari na wannan aikin wanda hakan ya sanya aka samu  sauki na ragowar cinkoso.

Ya kara da cewar sai kuma manyan hanyoyin da suka ratsa tsakiyar Nijeriya wadanda a halin yanzu gwamnatin ta raiya ke gudanar da gyare-gyarensu. Muna fatan gwamnati za ta ci gaba da gudanar da wadannan ayyuka domin jama’ar kasa su ci gaba da amfana.

Dangane da direbobin da suke yin amfani da kwayoyi masu sanya maye a wajan tuki domin biyan bukatarsu ta tuki musamman idan dare ya yi, sai ya ce babu shakka an samu wannan matsala a shekarun baya da suka wuce amman a halin yanzu an wuce wurin in ji shi, domin direbobbin yanzu arziki suke nema domin

A karshe, Kazaure ya ce ya yi alkawarin taimawa Alhaji Shehu Usman sampam wajen gudanar da shugabancin kasuwar Mile 12 tare da sauran sabbin shugabannin kasuwar.

Exit mobile version