Muna Son Buhari Ya Dauki Mataki Kan Maciya Amanar APC – Hon. Kibiya

HON. YUSUF ADO KIBIYA tsohon dan siyasa ne, wanda ya rike makamin Kwamishina a shekarar 1999 zuwa 2003 a tsohuwar Gwamnatin jihar Kano, kuma yana daya daga cikin Dattawan Jamiyar APC mai fada aji a siyasar Kano ta kudu da Nijeriya baki daya. Haka zalika, yana daga cikin masu kishin APC da son ganin ta cigaba da mulkin Nijeriya a cikin samun adalci da daidaito a Jamiyarsu da kuma samarwa ‘yan kasa abinda suke bukata na rayuwa. A wannan hira da ya yi Wakilin LEADERSHIP A YAU, MUSTAPHA IBRAHIM TELA, ya jawo hankalin masu ruwa da tsaki don ceto APC a yau. Ga dai yadda hirar ta kasance da shi a birnin Kano:

 

Duk da kasancewarka daya daga cikin dattawa a Jam`iyar APC an ji ka yi shiru a siyasance kwanan nan. Shin mai ake ciki ne a halin yanzu?

Kamar yadda kasani cewa ita siyasa ko muamala da a kayi to yana da kyau ka tsaya ka zuba ido kaga yadda zata kasance ko kuma mai za ayi bayan a matsayinka na dan siyasa wanda ya ba da gudinmawa yadda ta kamata domin yanzu ita siyasa ta zama kamar wasan yara ne idan kayi lakari da yadda abubuwa ke faruwa a cikin wannan siyasa ta wannan lokaci na yin wani abu da ba shi ya kamata ayi ba domin ita kanta siyasa kamar aikin gaiya ne da akeyi musamam a da can to itama haka ne sai ya kasance kamar ka zo an yi shuka da kai, an yi noma da kai an yi girbi da kai an yi casa amfani gona da kai har ta kai anyi abinci da gudinmawarka amma bayan komai ya kammala za a ci gajiyar aikinka, sai a ce ba kai a ciki, to ka ga ansamu rudu kenan, an kuma samu cin amana kenan ako wacce irin tafiya akayi irin wannan sai muce Allah ya sawake!. Wannan ce ta sa mu kai shiru sai yanzu dan a gyara.

 

Ranka ya dade, mai ka ke nufi da cin amana a siyasance?

To kamar yadda na fada ne ai na ce kasan a lokacin zabe kowa ya fito ya ba da gudimawarsa wani tatinani wani kudi wani iliminsa lafiyasa wani kuma duk ya yi amfani da abunda yake da shi dan dai akai gaci ayi nassara kuma anyi nassara kuma wannan abu kamar abunda ake cewa Hayi ne wato kan daki ko Jinka, da ake fara yinta tun ranar laraba ko Alhami wanda kafi a sako daga sallar jumaa an kamala wanda da an dawo daga sallar Jumaa Jama`a sun taru sai kawai a durata tu nasarar siyasa sai an taro ake samunta kuma kowa zai zo ne da kyakyawar niya in an ci shi ma ajawushi cikin Gwamnati dai dai matsayinsa yadda zai cigaba da ba da gudumawarsa ta yadda za ayi nasara a tafiyar tun da ya sha wiya ya san irin fadi tashin da akayi har aka samu Gwamnati to amma da ta samu sai aka manta da shi wanda aka nema da shi aka samu sai aka je can waje aka dabo wanda basiyi wahalar kumai ba aka basu mukami akeyi da su kai kuma amanta da kai harma ka zama abokin gaba saboda jagora ko shugaban tafiya bayasan gani fuskarka to kaga mai za kira wannan in ba cin amanaba sabo da haka ita kuma kasan amana duk wanda yaci amana sai yayi nadama kuma sai yayi ta mai zubar da kudi to nidai wannan shi ne abunda nake nufi da cin amana kuma wannan dabia ta gwurbata siyasa sosai.

 

Amma ana ganin cewa kai da ka fito daga kano ta kudu in ana maganar cin gajiyar siyasar Jam iyar ku ta APC ai kunci ganin yadda kuka samu titi tun daga titin zuwa Ziriya har zuwa Garko da dai sauran ayuka da kuka samu a shekaru shida na wannan Jam`iyar ai an biyaku ko?

To kai dan Jarida kana maganar kano ne kawai ko? Ni ina magana ne a matakin Jaha da na kasa baki daya ma ana kasa da sama dan haka jam`iyar APC ta samu a wannan matsala ta mantawa da wadanda su ka wahalta mata, to kuma kasan wannan dai matsala ne babba a tafiyar siyasa da ake cimma nasara.

Kuma mu koma Maganar aiki da kayi a tambayar ka ni dai ina maganar siyasa ne ba ina maganar aiki ba ne in kuma kana maganar aiki ne sai muyi ta ni maganar siyasa na ke da yadda muka samu kan mu a wannan yanayi na mulkin Jamiyyar mu ta APC a siyasance. To ma ita kan ta maganar aiki ai ba wani abu ba ne dama duk wanda aka zaba ai dan ya yi aiki a ka zabe shi kuma a siyasa ta Ilimi da Alummar da suka san abunda su ke yi in ka yi aiki ai da ma shi ne abun da yakamata ka yi kuma kudin Al`umma ne akai aiki da su ba na Aljihun ka ba saboda haka tafi ko yabo gaira babu dalili dan wanda aka zaba ya yi aiki ni a ganina kamar Jahilci ne ko ma ince Jahilci ne kai tsaye a irin wannan siyasar ta mu ta yanzu.

 

To ganin yanzu an rushe tunanin shugabanin jam`iyar APC ta kasa, ko ba kumai dai akwai sake habe kuma kana daya daga cikin Dattawan APC a kano, menene shawarar ka ta gyara tafiyar?

To shawarata ita ce a tsaya ayi adalci a tsaya doran gaskiya ka da abi san rai ko abu ranka bayaso indai gaskiya ne to ka tsaya kanshi amma ba a maida jamiya kamar kamfani ba sai abun da wani yake so za ayi wannan ba tafiya bace ta gaskiya tafiyar gaskiya shi ne adalci kuma shi ne babar mafuta daga matsalolin da suka dabaibaye wannan jamiya tamu ta APC kuma shi ne mukeso a tsaya ayi gyara wadanda aka batawa aka manta da su a jahusu a jika kamar yadda ta kamata kuma komai za ayi a duba cancanta da tsayuwar gaskiya kuma shi ne abonda mukeso duk wani mai kishin aluma mai kishi kasa yasan wannan matsala tun daga kan mai katin jamiya har zuwa shugaban kasa Muhammadu Buhari abunda muke so ya sani kenan kuma ya yi kokarin kawo gyara a wannan jamiya ta APC kai harma da yanayin kasar da sauran aluma kowa ya dau matakin tabatar da gaskiya da rukon amana ako wane irin al amari wannan shi ne shawarata ga shugabani jam`iya harma da wanda baya siyasa yasa gaskiya amana kishin kasa adalci da duk wani abu mai kyau a ransa shi ne shawarata.

 

Shekaru shida jam`iyarku ta APC na mulki a Nijeriya, shin ko akwai wani tsokaci a matsayinka na Dattijo?

Tsokaci shi ne gazawar jamiyar PDP ne a shekaru 16 da tayi tana mulki a kasarnan yasa aka tashi dare da rana ana adua ana fafutika ta neman sauyi Gwamnati a kasa kuma Allah ya kawo sauyi to abun tambaya shi ne an samu sauyin? In an samu shi kenan to APC tafi PDP in kuma ba a samu ba to PDP da APC abu guda kenan kuma abunda muke so shi ne jamiyarmu ta APC ta tashi tsaye wajan kyautatawa yayanta dama sauran yan Najeriya baki daya in tayi ada to ta kara in kuma batayi ba to tayi domin mai suma aikin alkari baya kamara kuma duk wani mai san cigaban jamaa to a tayashi da adua yaga ya yi nasara wannan itace nasarar al`uma baki daya.

 

A karshe, Hon Yusuf Ado Kibiya duk da gazawa da kake ganin jamiyarku ta APC ta yi a nan kano, a makon da ya wuce anyi zaben kananan hukumomi inda jamiyar APC ta cinye baki daya, shin baka ganin wannan cewa Jama`a sunyi na’am da ita?

To, ni dai a matsayina na daya daga cikin dattawan APC na ce ba zanyi wannan zabe ba bankuma yi ba dan ni in ganin ko inyi zabe ko karnayi aikin gama ya gama domin ko a zaban curo ko na fud Gwani ba mu gamsu da shiba kuma duk wani mataki na sulhu ko na a gyara ba mu samu nasara ba dan haka muka hakura da zaban burinmu dai ayi gyara saboda rashin gyaran zai sa mu tsinci kanmu a wani abu daban a wannan Jam`iya Allah ya sawake Amin.

Exit mobile version