Abba Ibrahim Wada" />

Muna Son Mbappe Da Neymar, Inji Real Madrid

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Thomas Tuchel, ya bayyana cewa kowacce kungiya tana son ‘yan wasa Kylian Mbappe da Neymar saboda kwarewarsu a kwallon kafa.
Kociyan ya bayyana hakane a lokacin da yake mayarwa da shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Florentino Perez martani bayan da ya ce Real Madrid tana zawarcin ‘yan wasan guda biyu na PSG.
A jiya ne shugaban gudanarwar Real Madrid ya bayyana cewa idan so samu ne kungiyarsa ta samu duka Mbappe da Neymar a domin kociyan kungiyar Zinedine Zidane yana son aiki dasu gaba daya.
Real Madrid dai ta dade tana zawarcin Neymar da Mbappe sai dai dawowar mai koyarwa Zidane yasa kungiyar da sake dawowa da neman ‘yan wasan wadanda take ganin idan ta same su za ta gyara matsalolin da suka addabeta.
“Ba wani abu bane domin kusan kowa yana son Neymar da Mbappe da Berrati da Markuinhos a kungiyarsa saboda manyan ‘yan kwallo ne amma abin farin ciki duka a kungiyarmu suke saboda haka kowa yanada damar da zaice yanason dan wasanmu” in ji kociyan na PSG
Sai dai a karshe ya bayyana cewa bazasu taba amincewa su rabu da manyan ‘yan wasansu ba saboda suma bazasu samu irinsu ba idan suka siyar dasu kuma duk kungiyar da take tunanin za ta samesu tana batawa kanta lokaci ne kawai.

Exit mobile version