Daga Shehu Yahaya, Kaduna
kungiyar kwadago ta kasa reshen Jihar Kaduna (NLC) ta nuna damuwarta dangane da Matakin da gwamnatin jihar ta dauka na korar ma’aikatan kananan hukumomin jihar haka siddan.
kungiyar ta ce korar da gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna el-Rufai tayi na kori ma’aikatan ba bisa ka’ida inda tace ya sabawa hakkin bil-adama.
A wani taron manema labarai da kungiyar ta yi a Kaduna ta bayyana cewa korar ma’aikatan ya saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 wanda ya tanadi hanyoyin da ake bi wajen sallamar ma’aikata, da gwamnatin ta yi watsi da su.
Da yake gabatar da jawabinsa, shugaban kungiyar ta NLC kwamared Ayuba Suleiman, ya ce matakin da Gwamnatin Kaduna ta dauka na korar ma’aikata ta yi wa dokar kasa karan tsaye, inda ta kori ma’aikata sama da guda dubu ba tare da biyansu hakkokinsu ba da kuma bin dokokin tsarin daukar aiki da sallamar ma’aikaci.
Ayuba Suleiman, ya kara da cewa duk ci gaban da Gwamnatin Kaduna take ikirarin cewa ta samu, an samu nasarar ne bisa irin jajircewa da hazakar ma’aikata amma ta rufe idanunta ta kore su daga bakin aikin.
Shugaban ya yi tir da kakkausar murya wajen bayyana jimaminsu a kan korar ma’aikatan wanda da yawansu ma’aikata ne na kananan hukumomi.
A ranar Talata 6 ga wannan watan gwamnatin Jihar Kaduna ta bayar da sanarwa korar ma’aikata sama da guda dubu daga bakin aikinsu bisa abin da ta kira yi wa tsarin aikin gwamnati garambawul, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce daga galibin al’ummar jihar.