Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Muna Yaba Wa Gwamnatin Tarayya Bisa Inganta Asibitoci – Farfesa Jika

by
1 year ago
in LABARAI
3 min read
Asibitoci
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Daga Mustapha Abdullahi,

Shugaban da ke kula da babban asibitin masu fama da matsalar kwakwalwa na Gwamnatin tarayya da ke Kaduna, Farfesa Abdulkareem Jika Yusuf, ya bayyana farin cikinsa da jin dadinsa da halin da asibitin yake ciki sakamakon samun aikace-aikacen bunkasa babban asibitin domin amfanin jama’a.

Farfesa Abdulkareem Jika Yusuf, ya dai bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna, jim kadan bayan an kammala zagayawa da su domin ganin irin yadda aikin ci gaba yake gudana a daukacin harabar asibitin.

Labarai Masu Nasaba

‘Yan Bindiga Sun Fille Kan Wani Dan Majalisa A Jihar Anambra

’Yan Bindigar Da Suka Sace Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Nasarawa Sun Sako Shi

Kamar yadda Farfesan ya shaida wa manema labaran bayan sun gane wa idanunsu irin yadda ayyuka ke gudana, ya bayyana cewa a halin yanzu Gwamnati ta kara wuraren kula da lafiyar jama’a da a can baya babu su.

“Kamar irin wurin wankin koda, babban wurin Gwaje-gwajen gano cututtukan da ka iya samuwa ko nan gaba da ba a sansu ba da kuma wurin ajiye masu dauke da cutar Korona da cututtuka makamantan hakan, duk yanzu ga su an samar da su a dan kankanin lokaci”, Inji Jika Yusuf.

Kamar dai yadda aka zagaya da manema labaran sun gane wa idanun mu sababbin Injunan zamani masu inganci kirar kasar Italiya huda (4) domin wankin koda ga masu fama da matsalar ciwon koda, kuma ana yin amfani da du wajen duba yanayin jinin jikin mutum.

Sannan mara lafiya zai iya yin amfani da Gado ko kuma ya zauna a kan kujera da wata na’ura a hannunsa, ya kwanta ko ya dan kishingida idan ana yi masa wankin Kkodar, Sannan babu maganar dauke wuta domin akwai manyan na’urorin da za su ajiye hasken wutar lantarki tsawon lokaci idan ayi ta amfani da Injunan wankin kodar, kamar yadda wani babban jami’in kamfanin SUDABELT da ke aikin Sanya Gadaje, Injunan zamani ya shaidawa manema labarai lokacin da suka kai wannan ziyarar domin ganewa idanunsu irin ci gaban da aka samu a asibitin.

Mun kuma ga Gadaje irin na zamani masu amfani da na’urorin zamani wanda mara lafiya ko Likitoci ko masu aikin jinya za su iya yin amfani da su domin a dago mara lafiya idan ya na kwance, nan ma ba batun maganar ba wutar lantarki domin akwai na’urorin ajiye hasken wutar lantarki a samu wutar a ko da yaushe.

Kuma duk wadannan gine ginen da na’urorin kula da kiwon lafiya na zamani an samar da su ne a kasa da watanni biyu kamar yadda wani jami’in asibitin ya shaida mana.

An kuma kai mu har cikin dakin ajiyar kayayyakin asibitin wanda katafaren wurin ajiya ne mun kuma ganshi makare da kayayyaki irin na zamani duk za a Sanya su a wuraren da ake kokarin kammala ginin a halin yanzu.

Mun kuma zagaya inda Farfesa Abdulkareem Jika Yusuf ya kara gina sababbin ajujuwa domin karatun dalibai da ke neman ilimin kwarewa wajen fannin kwakwalwa, domin mun ga dalibai da muka yi magana da su suka shaida mana cewa sun zo ne daga Gwagwalada Abuja za su yi karatun sanin makaman aiki na sati biyu, an dai kammala Ajujuwan an Sanya kujerun zama da Tebura a cikin Ajujuwan.

Kuma mun ganewa idanun mu aikin gina dakunan kwanan dalibai na makarantar da ake gina wa a halin yanzu dakunan kwana guda Arba’in (40).

Mun kuma ga inda ake gina babban katafaren wurin zaman marasa lafiya irin na alfarma ga duk wanda ya samu kansa cikin halin damuwa,tabin kwakwalwa da dai irin matsalar da asibitin kan iya magancewa, ana ginin alfarma domin biyan bukatar jama’a.

Akwai kuma wani ginin da shi ma an kusa kammala shi da za a ajiye marasa lafiyar kwakwalwa wanda ba batun mara lafiya ya ce zai ta fi gina don kawai ya na samun sauki, wanann Ginin an kusa kammala shi ayi bikin budewa.

Mun kuma ga sababbin motocin daukar marasa lafiya da asibitin ya sayo manya manya irin na zamani da ke dauke da duk abin da ake bukatar a samu a wadannan motocin domin kula wa da marasa lafiya.

An kuma kammala ginin wurin kula wa da marasa lafiya na gaggawa wanda katafaren gini ne bene, ha kuma babban ofishin gudanar da mulki da babban wurin masu ilimin sanin Magunguna da duk an kammala wurin a halin yanzu sai batun fara amfani da shi kawai ya rage.

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Tabbatar Da Kama  Wasu Sojoji Masu Hulda Da ‘Yan Ta’adda

Next Post

Ramadan:  Nasarorin Da Ake Samu A Watan Azumi Na Da Tasiri Da Gudummowr Mata – In Ji Dakta Zainab Bagudu

Labarai Masu Nasaba

‘Yan Bindiga Sun Fille Kan Wani Dan Majalisa A Jihar Anambra

‘Yan Bindiga Sun Fille Kan Wani Dan Majalisa A Jihar Anambra

by Abubakar Abba
41 mins ago
0

...

’Yan Bindigar Da Suka Sace Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Nasarawa Sun Sako Shi

’Yan Bindigar Da Suka Sace Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Nasarawa Sun Sako Shi

by Leadership Hausa
2 hours ago
0

...

Wani Bene Ya Kuma Ruftawa Ya Danne Mutane A Legas

Wani Bene Ya Kuma Ruftawa Ya Danne Mutane A Legas

by Leadership Hausa
3 hours ago
0

...

 ‘Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 360 Da Sace 1,389 Cikin Watanni 3 A Kaduna

 ‘Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 360 Da Sace 1,389 Cikin Watanni 3 A Kaduna

by Muhammad Bashir
3 hours ago
0

...

Next Post
Azumi

Ramadan:  Nasarorin Da Ake Samu A Watan Azumi Na Da Tasiri Da Gudummowr Mata – In Ji Dakta Zainab Bagudu

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: