Sunusi Alhaji Mustafa da aka fi sani da Sunusi dan Alhaji, ya bayyanawa wakilinmu RABIU ALI INDABAWA dalilansu na yada manufofin Sanata Rabiu Kwankwaso. Dan Alhaji ya bayyana hakan a matsayinsa na shugaban kungiyar darikar Kwankwasiyya na Katampe dake Abuja, ga dai yadda hirar ta kasance
Da fari masu karatu za su so sanin sunanka da tarihinka a takaice
Salamu alaikum, ni sunanan Sunusi Alhaji Mustafa, amma an fi sanina da Sunusi dan Alhaji, ni dan garin Malamawa ne dake Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano, na yi karatun Firamare a garin Malamawa daga nan na je makarantar Sikandire ta garin Kutama, sannan Allah ya bani dama na halarci Kwalejin Kur’an dake Salahawa a Karamar Hukumar Gwarzo, daga kuma karatu bai yi nisa ba.
To ana kiranka shugaba, me kake shugabanta?
To a cikin hakan ne muka ga shugabanci irin na Mai Girma Rabiu Musa Kwankwaso da muka gani a Jihar Kano, wanda a lokacin mun kafa kungiya ne a domin aikin Kanfen na gwamnan Jihar Kano, kuma cikin yardar Allah sai muka yi nasara ya zama gwamna. Sannan dukkan bangarorin rayuwa, daga aikin yi masa’antu makaranta, aikin dogaro da kai da sauransu, daidai gwargwado mutane sun yaba cewa Rabiu Musa Kwankwaso jagora ne nagari.
To bayan mun yi nasara a nan sai muka fara tunani kuma a 2014 na takarar shugaban kasa ta sa, to an mun yi kokari a 2014 a jam’iyyar APC Allah bai ba mu nasara ba, Baba Buhari ya yi nasara. To da muka dawo muka cigaba da hada kan mutane, tun da shugaban kasa ne duk jihohin Nijeriya in dai mutum yana tare da Kwankwaso in dai shi mai kaunar sauyi ne, muka ce bari mu hada kungiyar da ba iya ‘yan Kano ba, Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya har ma da kasashen Inyamurai domin mu kara tallata dabi’u da halayya nagartattu na Mai Grima Kwankwaso da nuna abin misali a Kano, mutane su zo domin mu ne za mu gyara yau don gobe ta yi kyau.
Bisa ga wane dalili kuke son kara yada manufofinsa bayan kun ce ya yi an gani?
Dalilan suna da yawa, ciki akwai bangaren ilimi, duk al’ummar da ka ga ta kasa to ba ta da ilimi, duk al’ummar da take so gobe da jibinta su yi kyau, to sai ta ba wa bangaren ilim kulawa ta musamman, bangaren noma, idan babu abinci babu rayuwa, a nan ma ya ba da himma sosai wajen inganta wannan fanni, a wadata ‘yan kasa da abinci ba sai an zo ana shigo da kayayyaki ta wata hanya har ana karkashe jama’a ba. Idan da gwamnatinmu ta ba da kulawa kan harkar noma da ba a rika kamawa ana daure mutane har ta kai ga kisa ba.
Sai harkar lafiya, idan ka je asibitocinmu na kauye ka ga yadda mata suke bukatar agajin gaggawa yayin da za su haihu, idan cikin damina ne za ka ga dakunan da suke kwance babu rufi, kuma likita ma sai ya ga dama zai zo saboda alawus din da ake bashi bai ishe shi ba, to akwai bukatar shugaban da zai kula da wannan bangare. Dole a wadata su da kayan aiki da sauran abubuwan da suka kamata a kula da su, domin rashin hakan ne ake ta fama mace-macen mata a bangaren haihuwa, a lokacin Gwamnatin Kwankwaso tun daga haihuwar yaro har zuwa shekara biyu kyauta ne.
Sai kuma maganar wutar lantarki, Mai Girma Kwankwaso ya gina wutar lantarki daya a Challawa daya Tiga domin bunkasa masa’antu, domin gwamnati ba za ta iya daukar nauyin rayuwar mutane gaba daya ba, amma idan aka samar da wutar lantarki ita ce za ta samar da kashi 70 zuwa 80 na al’ummar kasa su samu aikin yi. Na gaba kuma shi ne harkar tsaro, idan ana adalci to babu rigima, an ba wane-an ba wane babu rigima, bangaren tsaron nan jami’an tsaron nan ba’a basu hakkinsu yadda ya dace, don haka jami’an tsaronmu suna fuskantar matsaloli akan sha’anin tsaro. Amma kamar yadda mai gidanmu ya rike mukamin Ministan tsaro na tarayyar Nijeriya, ka ga ya san harkar tsaro domin ya yi mu’amala da manyan jami’an tsaro na kasa, don haka muke ganin in ya samu nasara zai kula da harkar tsaro sosai.
Halin da ake ciki a yanzu idan ka tashi za ka je Kaduna daga nan Abuja ba karamin hadari bane, mu Kanawa ne, ga jirgin kasa ya gagari talaka, don haka muke neman shugaban da zai tsaya akan wannan al’amari don a samu gyara. wannan shi ne dalilinmu na tallata Mair Girma Kwankwaso a matsayin dan takararmu na shugaban kasar Nijeriya.
To shi shugaba kasa na yanzu matsalarsa ita ce rashin daukar shawara, sha’anin tsaron nan akwai masana kwararru har da abokan aikinsa sun bashi shawara akan abin da ya kamata ya yi bai yi ba, to mu namu shugaban mai daukar shawarar al’umma ne na kasa, zai ba wa tsaro kulawa ta musamman zai dauko wadanda suka karanci tsaro ta fanni daban-daban ya basu hakkinsu kuma ya sa ido a kansu. Don haka muna da tabbacin zai dauki shawara kan abin da ya kamata a yi akan tsaro.
Ga zabukan kananan hukumomi suna gabatowa a Jihar Kano, ya kake kallon yadda za ta kaya tsakaninku da APC?
Kamar yadda sanarwa ta gabata daga shugabanninmu na jam’iyyar PDP a Jihar Kano, cewa a hakura da shiga zabe, wannan ita ce matsayar al’umma. Mutanen nan mun ga yadda suke mun yi mu’amala da su, mun fahimci cewa bukatar su ce a gabansu ba bukakatar alumma ba, mu kuma bukatar al’umma ce a gabanmu. Idan aka ce hukumar zabe ta Jihar Kano ce za ta shirya zabe, ka ga dai abin da ya faru a zaben gwamna, wadannan abubuwa muka kalla kuma masana suka ba da shawara cewa a hakura ya fi zama alheri.
To amma an jiyo madugun Kwankwasiyya na cewa ba za su sake yarda da Inconclusibe ba ko a mutu ko a yi rai, ya kake kallon wannan batu a mahangar siyasa?
To ai wannan kalma ce irin tamu ta ‘yan siyasa, abin nan da masu iya magana ke cewa tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro. Dukkan doka mun bi mun shiga zabe, an gudanar da zabe ranar tara ga wata, dan takararmu Abba Kabiru shi ne a kan gaba, Inconclusibe kuma ai basu bari an yi zaben ba. Ka gane hikimar Kwankwaso ba wai Incoclusibe din bace haramun, da aka zo shin an bar mutane sun zabe ra’ayinsu? Abin da jagora yake nufi a nan shi ne ba zamu yarda da zalunci ba, ba zai yiwu mutane su yi zabe a shigo da wani daga bayan fage don a lalata nasarar da al’umma suka samu ba.
Kuma zaben kananan hukumomi da kake magana, idan ka kalli Jihar Kano idan har za a yi zabe su sun san baza su ci ba, Kwankwasiyya ita mutanen Jihar Kano suke yi, idan ka zo za ka yi zabe wancan abin ya faru a baya, to bai kamata a halin da ake ciki yanzu kuma a sake shiga wata sabuwar fitina a Kano ba. Don a zauna lafiya jagoranmu Rabiu Musa Kwankwaso ya ce a janye shiga zabe.
A karshe wane kira za ka yi ga ‘yan uwanka ‘yan Kwankwasiyya?
To kafin haka ina mika ta’aziyyata a madadina da iyalaina da kuma dukkan ‘yan Kwankwasiyya da muke nan Katampe Abuja da ma na duniya baki daya, ga jagoranmu Mai Girma Sanata Dakta Rabiu Musa Kwankwaso bisa ga babban rashi da muka yi na mahaifinsa, Allah ya jikansa ya gafarta masa, Allah ya aljanna makoma. Sannan ina mika ta’aziyyata ga Shugaban wannan Kamfani Sam Nda Isaiah, da fatan Allah ya baku hakurin rashinsa.
Sannan ina kira ga mutane masu daraja ‘yan Kwankwasiyya na jam’iyyar PDP, da mu yi aiki tukuru don mu gyara gobenmu, muna kiran ‘yan jam’iyyar PDP na Nijeriya bai daya, da su yi duba kan tafiyar jagora Mai Girma Rabiu Musa Kwankwaso a kaokarinsa na hada kan ‘yan kasa Musulmai da Kirista. Na gode.