Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home KIWON LAFIYA

Mura Cutar Dan Gata

by Muhammad
December 1, 2020
in KIWON LAFIYA
5 min read
Mura
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Idris Aliyu Indabawa

Cutar ita wata  cuta ce wadda wani nau’in nata majina zata rika zuba wadda ba mai kauri bace, wata kuma mai ruwa- ruwa ce, musamman ma kamar idan wanda ke fama da cutar ya yi atishawa. Cuta ce wadda a ke iya dauka daga wanda shi ya dade da kamuwa da ita cutar ta murar, wata ta na tare da yin Tari ne mai matukar wuya, wata kuma ciwon kai ne har ma da zazzabi ga kuma wayan jin kasala.

samndaads

A na ganin ba kamar wata babbar cuta bace, amma sai dai mutum ya kamu da ita zai iya ganwa. Wani nau’in na cutar Mura ana kamuwa da ita ce wata ta wanka da ruwan sanyi, yayin da kuma wani idan yayi wanka da ruwa na zafi sai ya kamu da ita, wannan kuma gwargwadon daga yadda jikin  mutum ya ke ne.

Wata Murar ta hanyar mu’amala da ruwan sanyi ne, har ma kwantar da mai fama da ita ta ke yi wani lokacin. Bugu da kari kuma cuta ce wadda a ke iya dauka ta hanyar cudanya.

Ga dai wasu bayanai nan gaba da za a rika haduwa da su wadanda wata masaniyar ilmim kimiyya Claudia Hammond dai ita ce wadda ta gudanar da bincke dangane da ta yi a kan ita cutar ta mura kamar haka:

Kamar dai yadda wasu suke ta maganar cewar idan muna Mura mu yi ta cin abinci, amma kuma ka da mu ci idan zazzabi ne mu ke yi, akwai alamun gaskiya ta wani bangaren. Tun da dai shi al’amarin na zazzabi ya kan dauki kwana daya ne ko biyu kuma ba ka jin dandano a tsawon shi wannan lokacin, cin abinci kadan ba wani abu ba ne wanda zai kasance mai wuya.

Ita mura kuwa ta kan dauki kwanaki tsakanin bakwai da kuma goma saboda haka kana bukatar cin abinci wanda kuma idan ba ka ci ba jikin ka zai yi rauni ko kuma kasance ba ka wani kuzari.

To, wannan ke nan al’amarin ya nuna wani abu ne da za a iya yi, to amma akwai wata sheda da ke tabbatar da cewar idan ka yi hakan za ka samu sauki da wuri?

Ba kayayyakin abinci na ruwa na da muhimmanci sosai kuma sune kayayyakin abincin da ke sa kwayoyin halittar jiki su yi aiki.

To amma kuma sau da yawa shirashin lafiya ya na sa mutum ya rasa dandanon bakinsa gaba daya, kuma an ce wannan rashin cin abinci na taimakawa wajen kara bunkasa garkuwar jiki.

To amma idan haka lamarin ya ke, me zai sa kin cin abinci ya jawo hakan a lokacin da ba mu da lafiya kawai.

Masana kimiyya na kasar Holland sun umarci wasu mutane da za su yi gwaji a kansu da ka da su ci abinci da daddare kafin so zo dakinsu na gwaji a jarraba su a lokuta biyu daban-daban.

A ziyararsu ta farko an ba su abinci na ruwa-ruwa, yayin da a karo na biyu kuwa aka ba su ruwa kawai.

Gwajin jinin da a ka yi mu su bayan sun ci abincin mai rwa-ruwa an gano cewa sinadarin (gamma interferon) da ke kara karfafa garkuwar jiki musamman mai yaki da kwayoyin cutar bairus (birus) mai sa mura, ya karu da ku san kashi 450 cikin 100.

Haka nan kuma a gwajin da a ka yi wa mutanen bayan sun sha ruwan kawai sai a ka ga raguwar wannan sinadari mai bunkasa garkuwar jikin.

A wani binciken kuma an gano cewa azumi ya na jawo karin wani sinadarin (interleukin-4) wanda mai kara garkuwar jiki har akalla linki hudu ne.

Fiye da karin da a ka gani bayan da aka ba mutanen abinci mai ruwa-ruwa su ka karya da shi bayan sun kaurace wa abinci da daddare.

Shi wannan sinadari (interleukin-4) ya na taka muhimmiyar rawar da yake takawa ne wajen yaki da cututtukan da kwayar bakteriya (bacteria) ke yadawa a jini da kuma tsoka.

Dangane da wannan abu da aka gano, idan mutum ya ci gaba da cin abinci kenan wannan ya nuna ke nan a lokacin da ya ke mura yana kara samun garkuwa daga kwayoyin cutar da ke damun mutum a lokacin da ya ke fama da murar.

Ta daya bangaren kuwa, shi zazzabi da kwayar cutar bakteriya ke jawo shi, rashin cin abinci ke nan shi kuma yana maganinsa, ta hanyar samun karin garkuwar jikin da rashin cin abinci ko azumi ke jawowa.

Wannan bincike na masana ilmin kimiyyar na kasar Holland ya bayar da madogarar da ake nema ke nan ga wadanda suka yarda da waccan maganar. Sai dai kuma fa abin ba hakan ya ke da sauki ba kamar yadda za a dauka ba ne.

Saboda haka ne idan a ka duba abin da yawanci ke jawo zazzabi mura ce, wadda ita kuma kwayar cutar bairus (birus) ke sanadiyar kamuwa da ita ta, ka ga ke nan shi wancan nazari bai yi daidai ba a nan.

Kuma shi hakan na rage musu yuwuwar yawan fitowar kurji a jikinsu. Idan kuma ana maganar hadarin kamuwa da Mura ne sheda ta nuna cewar, ya fi dacewa da su kananan beraye su fi cin abinci sosai.

Idan kuma mu ka sake dawowa akan mutane kuma, bincike ya nuna babu wata sheda ta kimiyya da ta jaddada wannan magana (cin abinci idan ka na mura, ko kuma zazzabi ne kuwa ka da ka ci abinci).

A fannin tarihin adabi da harshe ma, akwai muhawara sosai a kan asalin maganar, inda da yawa a ke cewa hatta a cikin tarin labarai na karni na 14 babu maganar.

Akwai maganganun ma da suke nuna cewar an sauya asalin yadda fassarar maganar ta ke ne.

SendShareTweetShare
Previous Post

Nijeriya Da Masu Zuba Jari Daga Waje Sun Cimma Yarjejeniyar Hakar Zinari

Next Post

Yadda Nau’in Irin Masara Na TELA Zai Samar Wa Nijeriya Biliyan N360 Duk Shekara

RelatedPosts

Warin Baki

Abubuwa Tara Da Suke Sa Warin Baki Da Yadde Ake Kauce Musu

by Muhammad
2 days ago
0

Cikin ko wanne lungu da kuma sako na fadin duniya,...

Yakar Yunwa

Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Naira Bilyan 1.8 Saboda Yakar Yunwa

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

A tsakanin 2017 da 2018 gwamnatin Nijeriya ta kashe akalla...

Sauro

Warin Kaji Na Iya Korar Jinsin Sauro Mai Sanya Cutar Maleriya

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Wasu masu bincike daga kasar Sweden sun gano cewar daya...

Next Post

Yadda Nau’in Irin Masara Na TELA Zai Samar Wa Nijeriya Biliyan N360 Duk Shekara

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version