Murar Tsuntsaye: Gwamnatin Tarayya Ta Harbe Kaji Sama Da 329,000

Daga Abubakar Abba

Gwmnatin Tarayya ta sanya an harbe sama da kajin gidan gona guda 329,000 a wuraren kiwonsu guda  62,  bayan barkewar  murar tsintsaye (HPAI) da ke ci gaba da zama barazana a daukacin wuraren kiwon kaji a fadin kasar nan.
In za a iya tunawa, tun a ranar 29 ga watan Janairu ne aka samu rahoton farko kan bullar annobar a shekarar nan.

Daga ranar 5 ga watan Janairu, kimanin kajin gidan gona guda 421,947 ne aka ruwaito sun harbu da annobar ta murar tsintsaye

Har ila yau kuma, kimanin kaji guda 92,422 ne suka mutu bayan sun harbu da cutar, inda cutar ta yadu zuwa kananan hukumi guda 20 a dake a cikin jihohi takwas.
Bayanai daga ma’aikatar aikin noma da raya karkara ta kasa, sun nuna cewa, a ranar 9 ga watan Afirilun wannan shekarar, ma’aikatar ta rage yawan kimanin kaji guda 329,556 a wuraren kiwo guda  62.

Dakta Adeniran Alabi, Babban Jami’in kula da lafiyar dabbobi  na kasa ya bayyana cewa, a shekaru biyu da suka gabata, Nijeriya ba a samu barkewar cutar ta murar tsintsaye ba.
Babban Jami’in kula da lafiyar dabbobi wanda kuma shi ne Daraktan dakile yaduwar cututtukan dabbobi a ma’aikatar aikin gona da raya karkara ya ci gaba da cewa, an samu bullar cutar ce a ranar 9 ga watan Janirun wannan shekarar inda aka tabbatar da barkewar annobar a  karamar hukumar jihar Nasarawa dake a cikin jihar Kano.
“An  samu bullar cutar ce a ranar 9 ga watan Janirun wannan shekarar inda aka tabbatar da barkewar annobar a  karamar hukumar jihar Nasarawa dake a cikin jihar Kano”.
Dakta Alabi ya yi nuni da cewa, ya zama wajibi a dauki matakan dakile yaduwar cutar da kuma bai wa masu kiwon na kaji da abin ya shafa diyya.
A cewar Babban Jami’in kula da lafiyar dabbobi  na kasa, Dakta Adeniran Alabi, mun fadakar da masu kiwon na kajin kan su dauki matakan da suka da ce, musaman domin a dakile yaduwar cutar zuwa sauran wuraren da ake yin kiwon kajin a daukacin fadin kasar nan.
Babban jami’in ya ci gaba da cewa, ma’aikatar aikin gona da raya karkara  na ci gaba da kai dauki a jihon da annobar ta bulla bisa binciken da aka gudanar a kwanan baya harda a wasu kasuwannin da ake sayar da kaji a kasar nan.

“Mun fadakar da masu kiwon na kaji kan su dauki matakan da suka da ce, musaman domin a dakile yaduwar cutar zuwa sauran wuraren da ake yin kiwon kajin a daukacin fadin kasar nan”.
Dakta Adeniran Alabi ya kara da cewa, barkewar annobar ta yanzu, ma’aikatar aikin gona da raya karkara  na kan yin aiki kafada da kafada da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC domin yin gwajin jinin kaji, musamman domin  a dakile yaduwar annobar.

“Ma’aikatar aikin gona da raya karkara  na ci gaba da kai dauki a jihon da annobar ta bulla bisa binciken da aka gudanar a kwanan baya harda a wasu kasuwannin da ake sayar da kaji a kasar nan”.

Exit mobile version