Isa Abdullah Gidan Bakko" />

Murna Ta Kama Sarkin Zazzau Bisa Ziyarar San Kano Gare Shi

Mai Martaba Sarkin Zazzau kuma Shugaban Majalisar Sarakuna na Jihar Kaduna, Alhaji (Dakta.) Shehu Idris, ya nuna matukar jin dadinsa ga Mai Martaba sabon Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kai ma sa tare da wasu hakimansa na masarautar Kano.

Alhaji Idris ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa yayin da San Kano ya kai ma sa ziyarar ban girma ta yini biyu a makon jiya.

Mai Martaba Alhaji Shehu Idris ya cigaba da cewa, wannan ziyara babu wata tantama, za ta kara yaukaka zumuncin da ke tsakanin Masarautar Kano da Masarautar Zazzau, wacce babu ya wanda zai iya bayyana yawan shekarun da wannan zumunci ke tsakanin masarautun ya fara.

Ya kara da cewar, saboda zumunci da kuma girmama juna da ke tsakaninsa da Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero (mahaifin Sarkin Kano na yanzu), musamman su ke yin zama na musamman tare, domin tattauna wasu abubuwa da za su ciyar da al’umma gaba ta fannonin ilimi da zamantakewar al’umma da kuma batun tsaro.

Wannan zama da su ke yi a tsakaninsu, a cewar Mai Martaba Sarkin Zazzau, su na yin sa ne a wani gari kusa da garin Paki, wanda Marigayi Sarkin Kano ne da kansa ya samar da wajen taron da su ke yi a tsakaninsu.

Saboda alakar da ke tsakaninsa da Sarkin Kano Ado kuwa, Sarkin Zazzau ya ce, a lokacin da ya dawo daga asibiti, ya ce, ya ziyarce a fadarsa, a nan ne ya yi murna da zuwansa tare da shaida ma sa cewar, tun da ya dawo daga asibiti, bai yi magana da kowa ba, bayan sun kammala gaisawa, a cewar Sarkin Zazzau, sai da ya rako shi kusa da motarsa. “Kwana goma da wannan ziyara Allah ya karbi rayuwarsa,” in ji Sarkin na Zazzau.

Tun da farko a jawabinsa, San Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce, ya ziyarci Mai Martaba Sarkin Zazzau ne a cikin fadarsa a matsayinsa da da uba kuma shugaba a gare shi, wanda ya bayar da gagarumar gudunmuwa ga cigaban ‘ya’yan Marigayi San Kano Ado Bayero na tarbiyyarsu da kuma duk wasu abubuwan da inganta rayuwarsu.

A nan ne kuma San Kano Aminu ya yi godiya ga Allah kan yadda Allah ya ba shi damar zama matsayin da zai zama mataki cikin mataimakan Mai Martaba Sarin Zazzau Shehu Idris, inda ya ce, biyayya da kuma girmamawa za ta cigaba da wanzuwa tsakaninsa da sarkin a matsayinsa na shugaba kuma uba abin jingina, domin samun ilimin yadda za a tunkari kowacce irin matsala idan ta taso a nan gaba.

A karshe, San Kano Aminu Ado Bayero ya yi addu’a ta musamman ga mahaifinsa da kuma sauran al’ummar Musulmi da addu’ar Allah ya kara wa Sarkin Zazzau Idris lafiya, domin saukin sauke nauyin da a ka dora ma sa.

Exit mobile version