Wakilinmu" />

Murtala Garo Jagora Ne Mai Kawo Cigban Al’ummarsa – Hon. Salisu Kabiru

Hon. Salisu Kabiru

Shugaban Karamar Hukumar Kabo, wanda kuma sh ne ya sake samun nasarar zabensa a karo na biyu, Hon. Salisu Kabiru Kabo ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa amsa kira na yin tururuwa wajen fita zabe ba tare da samun tashin hankali ko korafi na rashin kawo kayan aiki ba, musamman. Ya bayyana haka ne a zantawarsa da ‘yan jarida a garin Kabo.

Ya ce, duba da irin abubuwa da Gwamnan Kano, Ganduje ya ke kawo wa na alkhairi a Kabo, kamar yanda sauran masu madafun iko na Karamar Hukumar suke yi, wadada suka hada da Kwamishinan Kananan Hukumomi, Alhaji Murtala Sule Garo, shi ya sa da wahala a ce wata jam’iyya ta yi tasiri,shi ya sa ba su da haufin samun nasara da APC ta yi a zaben.

Hon. Salisu Kabir Kabo ya ci gaba cewa, daga irin muhimman ayyuka da suka mora, akwai aikin tituna a sassa daban-daban, haka a harkar ruwan sha, ba su damMatsala, yanzu sun samar da rijiyoyin tuka-tuka da sanya sola guda 28 da za a iya jan ruwa na akalla mita 1,500 daga inda rijiyoyin suke. An yi gine-ginen makarantu da asibitoci, mutane shaida ne na abubuwan da Gwamna yake yi a Karamar Hukumar Kabo na bunkasa cigaban kasa.

Ya ce, wadannan abubuwa na ayyuka da ake yi su zai dora a kai bayan nasarar da ya sake samu ta lashe zaben shugabancin Karamar Hukumar Kabo a karo na Biyu, tunda mutane sun gamsu.

Daga nan sai Hon. Salisu ya yi kira ga al’umma su ci gaba da bada hadin-kai da suke bayarwa, da ci gaba da yi wa Gwamna da sauran jagorori addu’o’i nagari da bada goyon baya domin shugaba ya sami natsuwar da zai ci gaba da kawo wa al’umma romon damakwaradoyya.

Hon. Salisu Kabir ya jaddada goyon bayansu ga jagorancin Kwamishinan Kananan Hukumomi, wanda shi ne jigo a siyasar Karamar Hukumar Kabo, wanda duk wani aiki na ci gaban al’umma da gwamnati ta yi a yankin na Kabo, shi ne sanadi ko dai ta kai-tsaye, shi ne ya kawo ko kuma albarkacinsa aka yi, saboda haka ba su da wani abu da ya wuce yi masa fatan alkhairi, domin godiya da baki ta yi kadan sai dai kawai su fahimci me yake so kawai ya zama shi suke yi, domin duk abin da ake yi a Karamar Hukumar Kabo, shi ne jigo, duk abin da ya ce a yi, shi ake yi.

“Da Murtala Sule Garo zai ce a kama gudu daga nan Kabo zuwa Daura, kawai mutanen Kabo za su kama gudu ne, in sun je sannan za su ji mene ne ya faru, saboda sun san mutumin kirki ne kawai da yake kawo musu da alkhairi ko yaushe”, a cewar Shugaban Karamar Hukumar ta Kabo.

Exit mobile version