Musulmi Su Kara Azamar Tallafa Wa Marayu – Farfesa Tajoddin

Tallafa

Daga Isa Abdullahi Gidan ‘Bakko,

An bukaci al’ummar musulmi da su kara azzama wajen tallafa wa marayu ta fuskoki da dama, ba lallai a lokutan watan azumi ba, duk lokacin da mutum ya fahimci marayan da ke kusa da shi, ya na bukatar tallafi, domin ya sami damar da gudanar da rayuwarsa, kamar yadda ma su iyaye ke yi.

Fitaccen malamin addininmusulunci kuma babban malami a cibiyar nazarin addinin musulunci da harshen larabci na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya mai suna Farofesa Tahir Tajoddin ya bayar da shawarar a lokacin day a amsa tambayoyin wakilinmu da ke Zariya kan muhimmancin tallafa wa marayu da kuma ire – iren tallafin da ya dace a rika yi wa marayu.

Farofesa Tahir ya ci gaba da cewar, musulunci bai ce sai a watan azumi ne kawai za a tallafa wa maraya ba, a cewarsa, ako wane lokaci, duk lokacin dad a maraya ke raye, ya na bukatar tallafin abububwanda zai yi amfani da su, domin inganta rayuwarsa nay au da kullun, kamar yadda duk wani mai rai ke bukata.

Game da ire – iren abubuwanda suka dace a rika tallafa wa marayu da su, a cewar shehin malamin sun hada da samar da abinci da abin shag a wadanda ke kula da maraya ko kuma marayun da kula da ilimin marayun da kuma kula da lafiyarsa, sai kuma tufafin da zai sa a jikinsa na yau da kullun, in har aka rungumi tallafa wa marayu da abubuwanda da aka ambata, babu ko shakka, maraya ko kuma marayu, ba za su rika tunanin sun rasa iyayensu ba, domin, kamar yadda Farofesa ya ce, bayan mutuwar mahaifinsa al’umma sun rungume  shi da hannu biyu.

Har ila yau, Farofesa Tajoddin ya tunatar da al’ummar musulmi das u rungumi tallafa wa marayu da dukiyarsu komi kankantar ta, kamar yadda ya ce, ba karamin lada wanda ya tallafa wa maraya ko marayu ke samu ba, a duk lokacin day a yi amfani da abin da ya mallaka ya tallafa wa maraya, a nan ne ya ce duk mai niyyar tallafa maraya ka day a dubi kankantar tallafin da zai bayar ko kuma yawan abin da zai bayar, abin bukata kawai shi ne, mutum ya tsarkake zuciyarsa ya bayar da tallafin domin Allah, ba domin al’umma su ce shi mutum ne mai tallafa wa marayu ba.

A dai zantawar da aka yi da Farofesa Tajoddin ya yi kira ga al’ummar musulmi da kuma kungiyoyin da aka kafa su domin tallafa wa marayu, da su mayar da hankalisu wajen samar da wata hanya ta koyar da marayu sana’o’in dogaro da kai da kuma iyayen marayun, wannan zai matukar tasiri, a cewarsa ga marayun da kuma ma su rikon marayun, su kasance ma su tallafa wa marayunsu da kuma kan su, ba ako wane lokaci, su na jirar  a ba su tallafi ba.

Exit mobile version