Musulunci Ya Amince Da Allurar Rigakafin Shan Inna –Sarkin Musulmi

Daga Abubakar Abba, Kaduna

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya qara tabbatarwa da alummar qasar nan cewar Allurar rigakafin cutar shan Inna bata da wata illa ga yara qanana da magance cututtuka shida masu saurin hallaka yara kuma addinin Musulunci, ya amince da yin rigakafin cutar.
Abubakar ya sanar da hakan ne lokacin da yake jawabinsa a shalkwatar Qaramar Hukumar Wamakko dake cikin jihar Sokoto lokacin gangamin yaki da cutar na qasa.
Ya ce,” Allurar ta shan inna da kuma sauran cututtukan dake sauran hallaka yara qanana kamar su qyanda da kwalara da tarin fuka da sauransu basu da wata illa ga yaran.’’
Sarkin Musulmi ya ci gaba da cewa,“ Likitocin duniya da kuma Malaman addinin Musulunci, sun amince da Allurar akan cewar bata da wata illa ga yara qanana.”
A cewar shi, “mun kuma amince da abin da suka ce, domin ba zamu bari a yi wa yaranmu abinda zai cutar da lafiyarsu ba.”
Alhaji Abubakar ya yi kira ga xaukacin ‘yan Nijeriya dasu karvi Allurar hannu bibiyu haka kuma mata masu juna biyu kada suyi sake, wajen zuwa yin awo da kuma zuwa sauran gwaje-gwaje da ake yi wa masu juna biyu.
Sarkin ya kuma qara jadda da ci gaba da bada goyon bayan masu riqe da muqaman gargajiya dake Arewacin qasar nan, akan yaqar cutar da kuma sauran cutttuka shida masu sauran hallaka yara a qasar nan.
A nashi jawabin a waurin taron, Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal, ya yabawa Gwamnatin Tarayya da Sarkin Musulmi da kuma sauran masu ruwa da tsaki, a bisa gagaruwar gudunmawar da suke badawa akan faxakar da iyayen na su miqa ‘yayansu don ayi masu Allurar cutar.
Tambuwal ya bada tabbacin cewar, gwamantinsa, baza tayi qasa a gwiwa ba wajen ci gaba da bada gudunmawa da goyon baya don cakkafe cutar baki xaya a jihar ta Sokoto da qasa baki xaya.
Gwamnan ya ci gaba da cewa, gwamnatinsa a shirye take don taga ta cika alqawurranta na dukkan yarjejeniyar data kulla a kan ko wanne fanni, harda fannin lafiya a jihar.
Ya yi nuni da cewa,“ shi yasa gwamnatin jihar, ta warewa harkar lafiya har kashi sha shida bisa xari a cikin kasafin kuxinta na shekarar
2017.”
Gwamnan ya kuma sha alwashin magance dukkan qalubalen da fannin lafiya ke fuskanta a da nufin qara bunqasa fannin a jihar.
Shi kuwa, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa na Matakin Lafiya ta Farko na Qasa da kuma sauran cututtuka da za a iya yaxa su, Sanata Mao Ohuabunwa, ya bayyana cewar Majalisar tana san rai wajen ganin cewar qasar nan ta fita daga cikin sahun sauran qasashen dake fama da cutar.
Shi ma Shugaban Kwamitin Lafiya na Majalisar Wakilai Mista Chike Okafor wanda Mataimakinsa Alhaji Mohammed Usman ya wakilta a wurin taron, ya bayyana cewar, kwamtin zaici gaba da sanya ido, don ganin ana tura kuxi a vangaren harkar lafiya a qasar nan, musamman don inganta lafiyar ‘yan Nijeriya.

Exit mobile version