Alkaluman mutanen da suka rasa rayukansu a wasu munanan hare-haren kungiyar ISIS a Syria sun kai kimanin 250 kuma akasarinsu fararen hula ne kamar yadda kungiyar da ke sa ido a kasar ta sanar a ranar Alhamis.
Farmakin na baya-bayan nan shi ne mafi kazancewa da aka kaddamar kan birnin Sweida tun bayan barkewar yakin basasa a shekarar 2011 a Syria.
Shugaban kungiyar da ke sa ido kan hakkin bil’adama a kasar Rami Abdel Rahman ya ce, kawo yanzu mutane 246 aka tabbatar da mutuwarsu kuma 135 daga cikinsu, fararen hula ne.
Sauran wadanda aka hallaka a farmakin sun hada da dakarun da ke goyon bayan gwamnati da mutanen da suka dauki makami don kare rayukansu a kauyukan da hare-haren suka shafa.
Abdel Rahman ya ce, akwai yiwuwar alkaluman su kara tashi nan gaba, lura da cewa, mutane da dama na fama da munanen raunin da suka samu.
Kungiyar ISIS ta fara kaddamar da hare-haren kunar bakin wake ne a birnin na Sweida kafin daga bisa ta kutse cikin kauyukan da ke Arewaci da gabashi, in da ta yi ta barin wuta da bindigogi kan mai uwa da wabi.
Akalla mayakan ISIS 45 suka mutu a yayin farmakin na ranar Laraba.