Daga Muhammad Awwal Umar, Minna
Akalla mutane 56 ne ake sa ran sun rasa rayukansu cikin 60 da ke cikin kwale-kwalen daukar kaya sanadiyar kifewar kwale-kwalen ya yi a kauyen kiri da ke karamar hukumar Munya a tafkin kaduna da ya ratsa jihar Neja.
Lamarin ya faru ne ga wasu ‘yan kasuwar jihar Kaduna da ke kokarin cin kasuwar Kwata da ke Zumba a karamar hukumar Shiroro. Wani da yake tabbatarwa LEADERSHIP A Yau yace lamarin ya faru ne sakamakon nauyin kaya da jama’a su kaiwa kwale-kwalen bayan anbaliyar da tafkin yayi nauyin ya rinjayi kwale-kwalen wanda ya janyo nutsewarsa nan take.
Kwale-kwalen yana dauke da fasinjoji a kalla mutum sittin da kuma kaya masu anauyi wanda mafi yawansu mata ne, zuwa hada rahotson dai ana sa ran mutane hudu ne kawai suka tsira da ransu yayin wda sauran kuma ana tsammanin ruwan ya ja su zuwa tafkin shiroro.
Babban Darakta a hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja, Alhaji Ibrahim Ahmed Inga, ya bayyana cewa kananan masunta sun fantsama don lalubo wadanda hadarin ruwan ya rutsa da su.
Ibrahim Inga ya kara da cewar a kowani lokaci suna jawo hankalin masu tukin jiragen kwale-kwale da su kauracewa daukar kaya wadanda suka wuce kima musamman ma a lokacin ruwa, haka kuma muna kira a gare su da su kansance suna anfani da rigunan kariya dan kaucewa ire-iren wadannan hadurran.