Mutane 656 Ne Suka Kamu Da Cutar Kyanda A Jihar Kebbi

Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta tabbatar da faruwar matsalar kamuwa da cutar kyanda ga mutane 656 da ake zargi sun kamu da cutar a kananan hukumomi 21 da ke fadin jihar.

Kwamishinan kiwon  lafiya ta Jihar Kebbi, Alhaji Usman Umar Kambaza, ya bayyana hakan ga  manema labarai a Birnin-Kebbi, cewa za a tura kungiyoyin masu yin allurar rigakafi guda dubu 1,131 don gudanar da allurar  rigakafi zagaye na biyu, domin a iya magance matsalar cutar kyanda a fadin jihar.

“Don magance wannan, jihar na shirin yakin  da cutar kyanda tare da goyon bayan Kungiyar Kula da kiwon Lafiya ta Kasa da sauran abokan hulda. Ana sa ran fara yaki da cutar kyanda  a ranar 26 ga watan Satumba, kuma kimanin yara dubu 898,174 ake sa ran za a yi wa allurar rigakafi a cikin jihar ta kebbi” in ji kwamishinan.

Hakazalika ya ce “Allurar rigakafin za a yi ta ne ga yara ‘yan watanni 9 zuwa shekara 5 na haihuwa, a kowacce karamar hukumar mulki da ke cikin jihar ta kebbi,”

Bugu kari , Kambaza ya bayyana cewa za a ajiye masu bayar da allurar rigakafi a wurare daban-daban a bakin gidajen mutane a mazabu 225 da ke jihar, inda ya kara da cewa “babu wata mace da za ta yi tafiyar da ta wuce fiye da kilomita daya don yin wa ‘ya’yanta allurar rigakafi.”

Daga nan Kwamishinan ya bukaci ‘yan jarida, hakiman gargajiya da shugabannin addinai, da sauran masu ruwa da tsaki don shiga cikin shirin tattara mata da masu kula dasu domin kaucewa yaduwar cutar kyanda, saboda haka a fito a karbi allurar rigakafi.

A daya bangaren kuwa, Babban Sakataren hukumar kula da Kiwon Lafiyar Jama’a na karkara ‘KBSPHDA’, Dakta Manir Jega, wanda ya kwatanta wannan adadi na wadanda suka kamu da cutar kyanda a kananan hukumomin jihar kebbi da abu marar dadin ji. Ya ce yawancin wadanda suka kamu da cutar, hakan ya faru ne saboda kin amincewa da fitowa  don yin allurar  rigakafi.

Dakta Manir Jega ya bayyana hakan ne a cikin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Birnin Kebbi, ya ce hukumarsa za ta tabbatar da cewa wannan matsalar ta bullar cutar kyanda ta faru ne sanadiyyar rashin fitowa da yara domin karbar allurar rigakafin a lokutan da ake ta yekuwar allurar rigakafi a shekarar 2016 da suka gudanar a cikin jihar ta kebbi.

Bugu da kari ya ce, “muna da matsalolin cutar kyanda guda 656 a cikin kananan hukumomi 21 da ke jihar, daga cikinsu akwai matsalar cutar ta kyanda 77 da aka tabbatar a cikin hukumomi 12 da kuma wadanda ke fama da cutar sankarau, amma hukumarsa ta yi iya kokarinta na ganin ta dakile matsalar ta hanyar bayar da magani da kuma allurar rigakafi, wanda yanzu haka sun warke kuma an sallame su,” in ji shi.

Exit mobile version