Mutane 90,000 Suka Amfana Daga Ayyukan Magance Cizon Sauro A Jihar Akwa Ibom

Daga Abubakar Abba

Sama da mazauna jihar Akwa Ibom su 90,000 a cikin shekaru suka amfana da kariya daga magungunan cizon sauro. Daraktan kungiyar na gudanar da shirin yaki da cizon sauro Dakat Patrick Adah ya sanar da hakan a kwanan baya a karamar hukumar   lokacin taron wayar da mutane kai da aka yiwa lakabi da  ‘Bikin Kirismeti da ingantacciyar lafiya’.

Ya ce, kungiyar ta kirkiro da na’urar yin gwajin ciwon  sauro da ake kira (Deki Reader) a cibibiyoyin kiwon lafiya talatin dake  Eket da Ibeno a cikin jihar.

A cewar sa, ayyukan da aka gudanar a kananan hukumomin biyu sun hada da yawan wayarwa da alumma kai da gudanar da gwajin ciwon da kariya da samar da magungunan cizon sauro da sauran su.

Daraktan yaci gaba da cewa, na’urar ta samar da alfanu sosai kuma abin dogaro ne wajen yin gwaji a cikin sauri kuma a yanzu haka, ana amfani dashi a kasar nan.

A cewar sa, na’urar tana kaucw wajen samar da kuskuren da dan adam zai  yi wajen yin gwajin sakamako.

Ya kara da cewa sakamakon gwajin, da aka yi na’urar (Deki Reader) ma’aikatar lafiya ta kasa da sauran masu ruwa da tsaki akan harkar kiwon lafiya sunyi na’am da ita.

Ya bayyana cewar yin amfani da na’urar, ana samun gamsasshen sakamako akan yadda za’a kare ciwon cizon sauro a kasar nan.

Ya ce shirin wanda aka gudanar dashi a kananan hukumomin biyu, kamfanin  EddonMobil ne ya dauki nauyin, a karkashin shirin kungiyar na yaki da cizon sauro.

A cewar sa,“munzo nan ne yau don wayar maku da kai akan cewar ana iya warkar da ciwon cizon sauro.”

Daraktan yace, “ mun zabi wannan lokacin bikin na kirismete ne don jin dadin lafiyar ku kuma muna godiya ga kamfanin na  EddonMobil a bisa samar da kudi ga shirin haka muna shawartar mutane dasu dinga amfani da gidan sauron da aka sanyawa magani in zasu yi barci da daddare.

Itama a nata jawabin a wurin taron, Darakta mai sanya ido da kididdiga dake hukumar yaki da cizon sauro ta kasa Dakta  Perpetual Uhomoibhi, ta jinjinawa kungiyar da kamfanin na EddonMobil akan hadakar da suka yi na yaki da cizon sauro.

Ta yi nuni da cewar hadakar ta jima tana taimakawa a shekaru da dama da suka wuce ta kuma yi kira ga sauran kamfanoni masu zaman kansu dasu taimaka don yaki da cizon sauro a kasar nan.

A cewar ta,“muna bawa kamfanoni masu zaman kansu kwarin gwiwa nasu taimaka wajen samar da kudi don yaki da cizon sauro a kasar nan.”

Ta yi kira ga kamfanin EddonMobil da ya kara tallafawa kungiyar ta Africare don ta karade sauran kananan hukumomin talatin da daya dake cikin jihar.

Shima shugaban karamar hukumar  Ibeno Mista Ifum Henry godewa kamfanin na  EddonMobil da kungiyar ya yi akan hadakar don yakar ciwoon cizon sauro a kananan hukumomin biyu.

Henry ya kuma yi alkawarin bawa kungiyar goyon bayan da ya dace  akan kiwon lafiya.

 

 

Exit mobile version