Gyaran jiki yana daga cikin sana’o’in da ke tashe a wannan zamanin. Adon Gari ya tattauna da wata kwararriya a harkar inda ta bayyana rashin hakurin mutane a matsayin babban kalubalen da take fama da shi a sana’ar. Ko yaya abin yake? Ga cikakkiyar hirar.
Da farko masu karatu za su so su ji sunanki da kuma zan takaitaccen tarihinki…
Sunana Rabi’atu Idris Suleiman kuma an fisanina da Badawee’s coollecton ko kuma Rabi Sule.
Ko zaki fazawa masu karatu zan takaitaccen tarinki?
An hafe ni a garin Sokoto, na yi makaranta a garin Sokoto na bar garin Sokoto a 2006 na koma da zama a garin Port-hacourt yanzu haka ina zaune a garin Bauchi waton Jihar Bauchi.
Shin kina ci gaba da karatu ne ko wata sana’a ko zaman gida kawai kike?
Ma sha Allah. Da farko dai ina karatu kuma ina sana’a. Karatun nawa dai ta sana’a nake yi, wato na cigaban sana’ata nake yi.
Kamar wacce irin sana’a kike?
Za ki kamar shekara nawa da fara sana’ar?
A Gaskiya zan kai shekaru Goma (10) haka da fara sana’a. Amma mutane sun san da ni bayan shekaru uku (3) zuwa hudu(4).
Me ya ja hankalinki har kika fara sana’ar?
Wallahi a duniya ni ba na son walakanci kuma ina son yi ma kaina komai sabodan ina da saurin fushi… Shi ya sa na daddage na nemi nakaina dan kar na ce a mun abin da bai kai bai kawo ba a mun wulakanci. Alhamdulillah Allah ya rufa asiri.
Kafin ki fara ita sana’ar da kike yi, shin kin nemi shawarar wasu dan neman sanin yadda ake yinta, ko zuwa kikai aka koya miki, ko dai kawai farawa kikai da kanki?
Gaskiyar maganan ita ce ni ina son kwalliya (makeup) saboda haka farawa nayi kuma daga nan na fara shiga mutane dan karin ilimi ta fannin kwalliya (makeup) kuma Alhamdulillah na koya na iya.
Ta yaya kika koyi ita sana’ar?
Ta wacce hanya kike bi dan ganin kin bunkasa kasuwancinki?
Alhamdulillah na bi hanyar buga flires wanda na rarraba wa mutane. Na gina sana’a ta hanyar yada shi a yanar gizo.
Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah na samu babban ci gaba sosai. Saboda an san sana’ar mutum kuma an san da zamansa. Haka cikin mutane za ka ji ana cigiyar badawee’s mai gyaran jiki. Ina haduwa da mutane daban-daban a silar sana’ar tawa.
Wanne irin kalubale kika taba fuskanta game da ita sana’ar, musamman ga su masu sayen kayan?.
A gaskiya babu sana’ar da ba ta da nata kalubale ni dai nawa kalubalen shi ne mutane ba su da hakuri a gyaran jiki saboda su sun fi son sha yanzu magani yanzu.
Akwai kuma har yanzu ina koya wa wadansu
Ahh, akawai su da yawa. Gaskiya ni ba zan iya tuna iya adadin mutanen da na koya wa kwalliya ba gaskiya.
Me za ki ce ga mata na gida musamman wadanda suke zaune kawai ba tare da wata sana’a ba, wacce shawara za ki basu?
Hmmmmmm.. Wallahi zama bai gan su ba, neman sana’ar hannu shi ne mafita, dan Manzon Allah (S.A.W) ya Albarkaci sana’ar hannu. Wallahi sana’a ce mafita.
Idan kika ci karo da matan da suke zaune a gida basa wata sana’a ya kike ji a cikin zuciyar ki?.
Ni dai babban burina shi ne a ce yau na malake babban wurin koya wa mata sana’a. Ina nufin mata kamar dari biyu (200) zuwa sama.
Wacce shawara za ki bawa mata na gida masu jiran miji?.
Wallahi sukan ba ni tausayi saboda zama da su a wuri ma babu wata karuwa. ‘So’ nakan zama mai ba su shawara a kan kama sana’ar hannu komin karancinta.
Ko akwai wani kira da za ki ga gwamnati wajen ganin ta taimakawa masu sana’a?
Eh gaskiya gwamnati na kokari a tallafawa mutane ta fannin koyar da sana’ar hannu. Sai dai masu koya su jajirce su yi ta yi.
‘Yan kasuwa muji tsoron Allah mu san kai mai sana’a kamar aminci da amana mutane suka baka. Ka yi koman ka tsakaninka da Allah ba karya da algushu a cikin kayanka. Sai ka ga Allah ya rufa maka asiri ya daukaka kayanka.
Toh gaskiya babban shawaran shi ne mu ji soron Allah komai za mu yi kuma mu zama masu gaskiya a fannin sana’armu kuma mu zama masu hakuri da jama’a, Allah ya taimake mu duk, amin.