Mutane Kalilan Ke Danne Arzikin Nijeriya -Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana takaicinsa kan yadda wadansu ‘yan tsiraru a kasarnan suke danne hakkoki mutane da dama wanda ke haifar da matsin tattalin arziki a kasar.

Shugaban kasa ya ce akalla mutane miliyan 150 ne ke cikin mawuyacin halin ni ‘ya su, inda suke hannu baka hannu kwarya.

Shugaban ya tabbatar da hakan ne a wani taro karo na 25 kan tattalin arzikin Nijeriya da yake gudana a birnin tarayya Abuja.

Taron an yi masa take da; wane hali Nijeriya za ta samu kanta a shekarar 2050?

Exit mobile version