Rabiu Ali Indabawa" />

Mutane Miliyan 224 Ke Fama Da Yunwa A Afrika – MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar Afirka na fuskantar bala’in yunwa ganin yadda yanzu haka mutane Miliyan 224 ke fama da karancin abinci mai gina jiki a nahiyar, sakamakon sauyin yanayi da kuma tashe tashen hankula.

Daraktan hukumar samar da abincin ta Majalisar Dinkin Duniya dake kula da Afirka Bukar Tijani, ya bayyana cewar halin da ake ciki yanzu haka, sakamakon abin fargaba ne, musamman ganin yadda ake saran adadin mutanen da ke Afirka zai kai Biliyan 1 da Miliyan 700 nan da shekara ta 2030.

Jami’in ya ce, rahsin abinci mai gina jiki ya karu daga kashi 21 a shekarar 2015 zuwa kashi 23 a shekarar 2016, yayin da adadin mutane dake fama da yunwa ya karu daga Miliyan 200 zuwa Miliyan 224.

Tijani ya bayyana sauyin yanayi da ambaliya da fari da kuma rashin ingancin abincin da ake nomawa a matsayin wasu daga cikin matsalolin dake haifar da yunwa.

Daraktan ya kuma bayana tashe tashen hankula a kasashen Somalia, Sudan ta kudu da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, a matsayin abubuwan da suka sanya matsalar yin kamari.

 

Exit mobile version