Mutane Miliyan 8.2 Kansa Ta Kashe Cikin Shekara Biyar A Duniya –Farfesa Adeyemi

Daga Idris Umar, Zariya

“Ba a iya daukar cutar kansa daga wani, kuma akwai tsammanin hauhawar yaduwarta sakamakon koyi da rayuwar yammacin duniya da kuma cikin al’ummar da suka manyanta. Wannan sanannen abu ne a tsangayata, inda ake samun Karin bulluwar cutar kansa kowacce shekara.” Wannan bayani ya fito ne daga bakin wani Farfesa a tsangayar ilimin amfani da haske wajen warkar da cututtuka (Radiology) a bangaren sashen ilimin lafiya (Faculty of Medicine) da ke jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, wato Farfesa Sunday Adeyemi Adewuyi, a wata lakca da aka shirya makon da ya gabata.

Farfesan ya Kara da cewa, “Cikakkiyar lafiya na da ginshikai

guda uku, wadannan ginshiKai kuwa sune a samu yalwarta, a samu dama ta iya biyan kudi domin ta, sannan a samu dama ta iya kaiwa gareta, to, cikon na hudun kuma idan wadancan sun samu, muna iya cewa dawwamar hakan. Amma a Nijeriya, da akwai nakasu a dukkan wadannan ginshiKan a bangaren lafiya wadda ta jibinci ciwon kansa.”

Farfesan ya bayyana cewa a yau in an ce mutum na da ciwon kansa a Nijeriya, to kamar an yanke masa hukuncin kisa ne, ba don komai ba sai don wajen samun maganinta ya yi karanci, ko kuma saboda marasa lafiyar ba su iya kaiwa ga maganin, in kuwa sun kai, to basu iya biya, bayan haka kuma har ma da wahalhalu da baKin cikin da marasa lafiyar kan fuskanta saboda rashin kulawar gwamnati, ma’aikatan lafiya, shuwagabannin asibita da kuma su kansu ma’aikatan lafiyan. Sai dai ya bayyana cewa za a iya samun ingantacciyar rayuwa bayan warkar da ita, saboda da dai ba wani da zai iya tserewa wannan cuta da ka iya zuwa ko da yaushe.

Kwararren masanin ya bayyana cewa ita dai wannan lakca an shirya ta ne da nufin ilimantar da mutane cewa in aka hada kai waje daya, za a iya yin abubuwa masu alfanu tare, kuma a fadakar da shuwagabanni da sauran jama’a akan irin tabarbarewar da harkar lafiya ta samu kanta ciki domin taimaka masu wajen zage damtse wajen ganin an samar da isassun kayan aiki, Kwararrun mutane da kula ta musamman kamar yadda ake buKata a duniya baki daya, da samun ingantacciyar rayuwa bayan warkar da cutar kansa.

Farfesa Sunday Adeyemi Adewuyi, wanda ya bayyana cutar kansa a matsayin wata cuta mai wuyar sha’anin gaske kuma wadda ke shafar jikin dan Adam ta hanyar girma mara tsari da KoKarin kutsawa sauran sassan jiki, ya Kara da cewa, “Alamomi ko abubuwan da ke nuna shigar kansa jikin dan Adam ba sukan bayyana bane daga shigar cutar, sai a hankali suke bayyana kuma tare da mummunar cutarwa a yayin bayyanar ga ayyukan jiki, sakin wasu abubuwa da kan haifar da canzawar lafiya, takurewa, rashin cikakken aiki daga bangarorin jiki, ragewar nauyin jiki, fitar jinni da kuma haifar da yaduwar cutar olsa da sauransu.” Sai dai kuma ya ce, “Wani abu mai muhimmanci shi ne, wasu cututtukan kansa ana iya gane su ta hanyar bincike kafin bayyanar alamomi, kuma yana da kyau a san cewa wadansu kuma kafin su fara bayyana, sun yi mummunar illa ga jiki har sun fi Karfin a shawo kansu.” Sai ya bayyana cewa, “Ilimantarwa game da cutar, aiwatar da bincike – bincike da kuma gano cutar da wuri na da muhimmin amfani idan muna son hana zuwa asibiti kan cutar latti, yaduwar cutar da kuma yawan mace – mace a inda muke rayuwa.”

Sai ya Kara da cewa, “Bincike dai ya nuna cewa a wannan bangaren namu, yawan masu zuwa asibiti domin kansa da kuma wadanda ke zuwa domin ta a Kasashen da suka ci gaba akwai tazara mai yawa ba kadan ba. Dan kuwa bincike ya nuna cewa a Kasashen da suka ci gaba, suna da kashi 20 cikin dari na bullar cutar, kashi 20 cikin dari na mace – macenta, kashi 20 cikin dari na masu cutar da suka je asibiti latti da kuma kashi 20 cikin dari na wadanda suke da cutar har ta ta’azzara, to amma a Kasashen mu masu tasowa ciki kuwa harda Najeriya, akwai kashi 80 cikin dari na bulluwar cutar, kashi80 cikin dari na masu mutuwa saboda ita, kashi 80 cikin dari na wadanda suka je asibiti latti saboda ita, kashi 80 cikin dari na wadanda ke da cutar har ta ta’azzara, kai a taKaicema dai, kayan aikin kula da cutar, Kwararrun ma’aikatan kula da ita da kayan aikin kular na zamani a Kasashen da suka ci gaba suke, inda mu kuma muke da kashi 20 cikin dari, dukkuwa da cewa mun fi yawan masu cutar, wanda hakan babban hatsari ne ganin ga yawan cutar amma kuma ga Karancin kayan aikin shawo kanta.”

Ganin cewa mutane ya kamata su san me ke kawo wannan mummunar cuta, sai sanannen Farfesan ya kada baki ya ce, “To, abubuwan da ke kawo wannan cuta ko haifar da ita biyu ne; da akwai wadanda suka jibinci mazaunan mu, akwai kuma na gado. Kashi 90 zuwa 95 cikin dari na abubuwan da ke kawo kansa daga mazaunan mu suke, amma kashi 5 zuwa 10 ne kawai cikin dari daga gado. To, a bangaren mazaunanmu din, akwai dabi’un mu na zamantakewa, kamar yanayi ko tsarin rayuwa, yanayin abinci da Kiba mai yawa, shan giya da shan taba, haske mai lahani, damuwa mai yawa, rashin ayyukan motsa jiki, gurbacewar muhalli, sinadarai da sauransu. Don haka cutar kansa mafi yawanci ba gado bane, saboda haka ya kamata musan cewa duk da yake ba za mu iya kaucewa abinda muka gada ba, to amma za mu iya daukar mataki kafin bayyanarta ta hanyar bincikawa da wuri domin samun waraka ko kuma ta hanyar

kaucewa yaduwar wannan gadon. Abun dai baKin ciki ne a ce kansa na yaduwa ne musamman ta hanyar yanayin zamantakewar mu, kuma wadanda tabbas za mu iya magancewa. Canza wasu dabi’unmu na da muhimmin amfani wajen kare wasu ire – iren cututtukan kansa da dama.”

Har ila yau Farfesa Adeyemi ya bayyana cewa ita dai wannan cuta ba ruwanta da shekara, maza ko mata, yanayi ko kalar fata, yare, addini, matsayin ilimin mutum, arzuki ko jam’iyyar mutum, tana ruruwane saboda gado da kuma yanayin zamantakewa ko mazaunanmu, don haka ire – iren kansa na dangantaka ne daga waje zuwa waje a cikin Kasa daya, ko kuma daga Kasa zuwa Kasa.

Cutar kansa, wadda wani bincike da Globacan ta gudanar a shekarar 2012, sakamakon binciken ya nuna cewa akwai mutane miliyan 14.1 wadanda cutar ta bulla jikinsu, mutane miliyan 8.2 wadanda suka mutu saboda ita sai kuma mutane miliyan 32.6 wadanda ke rayuwa da ita (cikin shekara biyar da gano ta) a shekarar 2012 a duniya baki daya, a yayin da kashi 57 cikin dari (mutane miliyan 8) suka samu bullar cutar, kashi 65 cikin dari (mutane miliyan 5.3) suka mutu sanadiyyar ta kuma kashi 48 cikin dari (mutane miliyan 5.6) wadanda aka bincika cikin shekara biyar bullarta ke faruwa a Kasashen da ke tasowa ciki kuwa har da Najeriya.

A cewar Farfesan, “Matsalolin da ke fuskantar kula da ciwon kansa a Najeriya sun yi yawa kuma suna buKatar kulawar shuwagabanni cikin gaggawa, dan kuwa daga cikin su shi ne hauhawar cutar, rashin cikakken iliminta, rashin isassun kayan aiki, rashin isassun ma’aikatan lafiya domin kula da ita, hauhawar talauci, tsadar magunguna da kudin asibiti a bangaren kula da lafiya, sashen lafiya ba shi ne na daya da gwamnati ta sa a gaba ba, rashin wutar lantarki isassa dan kuwa janaretocin da ake amfani da su masu amfani da man dizil ba Kananan kudI suke buKata ba, da dai sauransu.”

Daga Karshe ya bayyana kadan daga cikin hanyoyin shawo kan matsalar kamar fadada wuraren kula da cutar a kowanne yanki na Kasar nan kuma a gina sabbi a manyan asibitocin jami’o’I ta hanyar shigowar gwamnati da tallafin kudI kamar yadda ta yi a bangaren cutur Kanjamau (HIB/AIDS), akwai buKatar Kara samun horo ga jami’an lafiya domin samun horo na musamman, musamman ma wadanda suka jibinci cutar kansa da kuma hada kai da sauran takwarorinsu na Kasashen da suka ci gaba, ma’aikatar inshorar lafiya ya kamata su dauki nauyin masu cutar kansa ta bangaren biyan kudin maganinsu, bincike – bincike, kulawa da kuma taimakon musamman, gwamnati ya kamata ta samar da cibiyoyin Kididdiga da kuma rijistar masu kansa a kowanne yanki Kasarnan domin sanin bulluwar ta domin ingantaccen tsarin tunkararta, shugaban Kasa ya kamata ya yi wani kwamiti domin ganin an samar da hanyar gaggawa wajen sauKaKewa masu fama da cutar wahalhalu, a kuma cire duk wata siyasa a bangaren kula da masu cutar da dai sauransu, sai kuma ya miKa godiyarsa ga mahalarta lakcar.

An yi taro lafiya an gama lafiya.

Exit mobile version