Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ta fitar da wani rahoto da yake nuna cewar, sama da ‘yan gudun hijira milyan biyu ke guje wa yaƙe-yaƙen da ake yi a ƙasshensu a sassan duniya, in da wasu daga cikinsu ke fuskantar matsi a ƙasashen Turai da Amurka.
Kwamishinan Kula da ‘yan gudun hijira na Majalisar Ɗuniya Duniya, Filippo Grandi ya ce, akwai ‘yan gudun hijira dubu 650 daga Ƙasar Sudan ta Kudu, sai wasu dubu 500Musulmi ‘yan Ƙabilar Rohingya na Myanmar waɗanda ala tilas suka guje wa gidajensu zuwa Bangladesh saboda yaddaa ake azabtar da su.
Grandi ya shaida wa taron mako guda a Geneva cewa, a wannan shekara da muke ciki kawai sama da mutane miliyan biyu da suka shiga halin ƙunci saboda guje wa wuraren da suke zaune, don neman mafaka a wasu wuraren.Grandi ya ƙara da cewa, mafi yawa kan isa wuraren da suka sami mafakan ne a tagayyare cikin rashin ƙosasshiyar lafiya ga kuma yunwa, yayin da wasu yaran aka raba su da iyayensu.A cewar Kwamishinan ‘yan gudun hijirar, ya zuwa ƙarshen shekarar da ta gabata, ‘yan gudun hijira miliyan 17 da dori ke ƙarkashin kulawar hukumar, amma daga bisani sun ragu domin wasu sun koma ƙasashen da suka fito.