Yusuf Shuaibu" />

Mutane Sun Kasa Zuwa Kan Gawar Wani Tsoho Bisa Tsoron Korona

A laboratory operator wearing protective gears runs tests on sample possibly infected with Covid-19 at the Henri Mondor Hospital in Creteil, near Paris, on March 6, 2020 as the novel coronavirus strain that erupted in China this year and causes the COVID-19 disease already left nine dead in France and made hundreds ill. - (Photo by Thomas SAMSON / AFP)

Wani mutum ya fadi a kan hanya kuma ya mutum har lahira a yankin Rasco kusa da tsohuwar garejin Oke Fia da ke cikin garin Osogbo ta Jihar Osun, inda mazauna yankin da masu wucewa a kan hanya wadanda suka ga mutumin lokacin da ya fadi su ka kasa zuwa kusa da shi, domin tsoron cutar coronabirus (Cobid-19).

Yayin da mutanen yankin su ke yin mamakin musabbabin abin da ya jawo har wannan tsoho ya mutu a kan hanya. Wasu ‘yan sanda daga yankin Dugbe da ke cikin garin Osogbo sun so wajen da lamarin ya faru, inda suka dauke gawar mutumin.
Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Yemisi Opalola, ya tabbatar da faruwar lamarin. Opalola ya bayyana cewa, ‘yan’uwar mutumin sun zo, inda suka bukaci a ba su gawar domin su burne ta.

Hakazalika, wani lamari makamancin wannan ya faru a yankin Olaiya shi ma dai cikin garin Osogbo, inda wakilinmu ya labarta mana a cikin ‘yan kwanaki da suka gabat. Mazauna yankin sun damu tare da tsorata da musabbabin mutuwar wadannan mutane guda biyu.

Exit mobile version