Rabiu Ali Indabawa" />

Mutanen Ghana Za Su Sha Ruwan Famfo Kyauta

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya bayyana cewar al’ummar kasar za su kwashe watanni 3 suna shan ruwan famfo ba tare da biyan sisin kwabo ba, a wani yunkurin saukaka musu radadin zaman gida saboda takaita yaduwar cutar coronabirus.

Shugaban ya kuma bai wa kamfanonin samar da ruwan da na samar da wutar lantarki da su tabbatar sun wadata jama’a a wannan lokaci.

A yayin yi wa al’ummar kasar jawabi, shugaban ya kuma sanar da tsawaita dokar rufe iyakoki na karin makwanni biyu saboda rahotannin masana kiwon lafiya da ke nuna cewar akasarin wadanda aka samu da cutar a Ghana sun fito ne daga kasashen waje.

Exit mobile version