Connect with us

RAHOTANNI

Mutanen Mazabar Kadisau A Karamar Hukumar Faskari Sun Koka

Published

on

Mutanen mazabar Kadisau dake cikin karamar hukumar mulki ta Faskari a jihar Katsina sun koka da sanatan su mai wakiltar mazabar Katsina ta kudu Funtua Zone a majalisar Dattawa ta kasa Sanata Alhaji Bello Mandiya.

A lokacin da wakilinmu yake zantawa da Alhaji Hassan Abubakar wanda yake mazaunin Kadisau ya shaida ma wakilinmu cewar Sanata Bello Mandiya ya nuna ko in kula ga mutanen Kadisau ganin yadda ‘yan ta’adda suka ziyarci kauyen Kadisau suka yi ta’addanci akayi asarar rayukan sama da mutum 60 a garin na Kadisau banda kone shaguna da ‘yan ta’addar suka yi da kwashe masu dukkan dabbobin su a kwanakin baya amma sanatan bai zo mana jaje ba kuma bai turo kowa ba har ya zuwa yau da nake zantawa daku ‘yan jaridu wannan abun bakin ciki ne kuma ya nuna bai damu da mutane ba kuma bai tausaya mana ba kuma ya nuna ko a jikin shi wannan abun mamaki ne kuma abin bakin ciki ne.

Alhaji Hassan ya cigaba da cewar babu wani gari ko kauye a karamar hukumar Faskari da ‘yan ta’addar basu je suka yi ta’addancin ba amma Sanata Bello Mandiya bai je ba ko ya turo wata tawaga ko da mutum daya don a zo a jajanta masu, zaben Mandiya sanata abin da na sani ne a garemu inji Alhaji Hassan, ya ce, a makon da ya gabata ne ya tura wadansu buhunan shinkafa da taliya aka kai sansanin ‘yan gudun hijira a Faskari, ya ce, bukatar mu ta farko ya zo jaje idan bai da hali tunda ya biya bukatar shi sai ya turo tawagar shi domin su zo mana jaje amma tunda ya gama biyan bukatar shi ta an zabe shi ba mutane bane a gaban shi.

Alhaji Hassan ya ce, suna mika godiyar su ga mai girma Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari domin shi ya zo mana jaje a Faskari da Dandume muna nuna godiyar mu ga mai girma Gwamnan abisa kokarin shi.

Alhaji Hassan ya cigaba da cewar dan majalisar su mai wakiltar kananan hukumomin kankara da Faskari da karamar hukumar Sabuwa a majlisar wakilai ta kasa dake Abuja Alhaji Murtala mai nauyi kankara shima bai zo mana ta’aziyya ba kuma bai aiko kowa ba wannan ya nuna cewar ba sun tafi Abuja bane domin wakiltar Jama’a a’a.
Advertisement

labarai