Mutanen Zogarawa Na Farin Ciki Da Makarantar Da Wakilin Dukiya Ya Gina

zogarawa

Daga Ibrahim Muhammad

 

An bayyana ilimi da cewa, shi ne ginshikin mataki na samun cigaba a duniya da samun  tsira a lahira wanda kuma sai an je makaranta ake iya samun ilimi, Ambasada Alhaji Yusuf Ibrahim Wakilin Dukiya, dan kasuwar musayar kudi ta WAPA ya bayyana haka a lokacin duba wata katafariyar makaranta da ya gina a garin Zogarawa don taimakawa bunkasa ilimin al’ummomin yankin.

Ya ce, kullum bukatar dan adam ya yi abu mai albarka ta koyi da magabata. Kuma ba za ka san Allah ka bauta masa ba sai anyi karatu.

Ambasada Yusuf Wakilin Dukiya ya ce, ya tsaya ya yi kokarin gina makarantar Allah ya bashi ikon kammalawa fatansa ‘yan baya da ake tare Allah ya basu damar dorawa a kai.

Ya ce, ba abinda zaka yi a matsayinka na Musulmi  shi ne ka gina aiki na alkhairi da zai amfani bayan bayanka ka gina rijiya ko dasa bishiya  ka gina dan’adam.Burinsa a wannan makaranta Allah ya bada wadanda zasu dora akan ginshikin da ya yi.

Wakilin Dukiya ya ce Mutane har tausaya masa suke da yake ginin makarantar amma shi ba wanda yafi tausayawa irin iyayen Yara don haka suji tsoron Allah su taimakawa kansu da ya’yansu da jikoki dan makarantar ta dore.

Ya ce Kwalejin da akayi mata sunada Kwalejin tunawa da Halima  Usman Zogarawa daya kunshi makarantar furamare da sakandire da sashin koyon Kur’ani da ilimin addini  dana renon yara ya mayarda sunan iyayene domin in Allah ya taimaka kan kafa rayuwarka saika waiwaya ka tuna baya na renonda iyaye suka baka  da tarbiya albarkacin sune  dan haka  kullum dan’adam tabi iyaye yabi Allah bazai tabe ba.

Shima Danzogarin Zogarawa Alhaji Balarabe Sulaimanu  ya bayyana wannan kokari da wakilin Dukiya ya yi na gina makarantar  abin jin dadi ne a matsayinsa na haifaffen garin Zogarawa  Kwalejin da ya yi zai amfani al’ ummar Zogarawa dana Dawakiji wannan ba karamin abin alkhairi bane.

Dagacin na Zogarawa ya yi kira ga jama’a masu hali suyi koyi da irin wannan kokari na Wakilin Dukiya su rika yin irin wannan  domin kauyukansu sunada bukatar irin wannan makarantu kamar a Nasarawar Zogarawa suna bukatar makarantar Islamiyya da Asibiti harma mutan garin sun sai fili dan a gina Asibiti amma har yanzu ba’a sami wanda zaiyi ba.

Alhaji Bslarabe Sulaiman ya ce, ilimi shi ne ginshikin rayuwa duk wanda bai da ilimi baida manufa.Iyaye su kulada ganin ya’yansu na zuwa makaranta akai-akai a rika bibiyarsu a tabbatar suna zuwa.

Al’ummar garin Zogarawa sun nuna matukar farin ciki da jin dadi bisa wannan ginin katafaren makaranta da Wakilin Dukiya ya gina mu su.

Exit mobile version