Connect with us

SIYASA

Mutum 160 Suke Neman APC Ta Tsayar Da Su Tarakar Kujerun Majalisar Jihar Bauchi

Published

on

Abdulkadir Lawan Gyangyan, sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC reshen jihar Bauchi, ya shaida cewar kawo lokacin da suka fara sayar da fom da kuma lokacin da suka rufe na ‘yan majalisun dokokin jihar Bauchi, ya zuwa yanzu mutane 160 ne suka nuna sha’awarsu da jam’iyyar ta tsaidasu domin neman kujerar ‘yan majalisun jihar Bauchi a zaben 2019 da ke tafe.

Gyangyan wanda ya bayyana hakan a jiya, sa’Ilin nan da ke hira da ‘yan jarida a Bauchi, yana mai bayanin cewar mazabu 31 ne kacal don haka a cikin ‘yan takara 160 mutane 31 ne kadal za su kasance masu shiga majalisa.

Ya ke cewa, “Muna da mazaba guda 31 a jihar Bauchi, kawo yanzu mun samu wadanda suka sayi fom din neman APC ta tsaidasu neman kujerun ‘yan majalisun jihar Bauchi sun kai mutane dari da sittin 160.

“A kowace maba mun samu mutane sama da uku sun sayi fom. Amma mazabar da ta fi kowace mazaba samun masu sha’awar neman wannan kujerar, ita ce mazabar Fali da ke karamar hukumar Alkaleri mai mutane 9, sai kuma mazabar cikin Bauchi mun samu masu sha’awar tsayawa takara su 8, sannan mazabar Azare da Madara da Cinede take biye, sai Misau mazabar Ciroma ita ma tana da ‘yan takara 8.

“Amma mazabar da suka fi karancin samun masu sha’awa mazabar Kirfi mai mutum 4, Itas mutum uku ne, Duguri ma hudu. Sannan akwai wasu wurare masu hudu da biyar,” Inji Gyangyan

Ya yi kari da cewa a cikin ‘yan takarar da suke neman shiga majalisar jihar Bauchi su 160 a zaben 2019, mata biyar ne suke nema, inda kuma basu samu wani mai fama da nakasa da ke neman wannan kujerar ba, “A mazabar Fali muna da mace guda, Bauchi, Zungur/Galambi da Miri muna da mace guda da take neman wannan kujerar, sannan a Ganjuwa muna da mata biyu, sai kuma mazabar Bogoro muna da mace guda daya da ake neman wannan kujerar ‘yar majalisar jihar Bauchi,” inji shi

Ya shaida cewar a halin yanzu jam’iyyar APC tana da ‘yan majalisun dokokin jihar Bauchi su 27 da suke kan kujerarsu a halin yanzu, “A cikin 27 wasu sun tsaya a kan kujerarsu suna nema kenan, wasu kuma sun ci gaba wasu kuma sun tsaya sun hakura da takarar gaba daya.

“Muna da ‘yan majalisun jihar Bauchi 7 zuwa 8 da suke neman kujera ta gaba,” Kamar yadda ya shaida

Abdulkadir ya bayyana cewar kawo lokacin da ke hira da ‘yan jarida suna tsumayar zuwan jami’ai daga babban ofishin jam’iyyar na kasa kan fara shirye-shiryen tantance wadannan ‘yan takarar da za su samu zarafin shiga a dama da su a babban zaben 2019 kan kujerun ‘yan majalisun jihar Bauchi.

Gyangyan ya shaida cewar tunin suka tura wa uwar jam’iyyar jerin wadanda suka yanki fom, “za a tantancesu, wadanda suka cancanci shiga zabe za a amince musu su shiga, wadanda basu cancanta ba kuma za a ce musu su hakura daga wannan kujerar,” Inji shi

Abdukadir Gyangyan ya bayyana cewar jam’iyyar APC ba za ta lamunci rashin da’a ga kowani dan takara ba, amma ya shaida cewar za su baiwa kowani dan takara zarafin shiga a dama da shi muddin bai kasance butulu wa jam’iyar ba.

Ya jawo hankulan masu sha’awar APC ta basu dama da cewar su sani a kowani mazaba mutum gudane don haka ya nemi su maida hankalu su yarda da kaddara a duk lokacin da wani ya samu nasara a kansu.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: