Mutum 442 Coronavirus Ta Kama A Nijeriya

Ya zuwa yanzu mutum 277 suke da cutar Coronavirus a Nijeriya, a yayin da cutar gaba daya ta kama mutum 442. Sai dai mutum 152 an sallame su sakamakon sun warke.

Cibiyar dakile cutuka ta Nijeriya, NCDC ta tabbatar da hakan a daren ranar Alhamis a shafinta na Twitter.

NCDC sun ce ya zuwa karfe 10:20 na daren 16 ga watan Afrilu, an samu karin mutum 35 da suke da cutar COVID-19 daga jihohi hudu inda aka samu mutum 19 a Legas, 9 a Abuja, 5 a Kano, sai kuma biyu a Oyo.

Cibiyar ta ce an salami mutum 152 a yayin da aka samu mutum 13 suka mutu daga cutar.

Ya zuwa yanzu dai cutar ta bulla a jihohi 20 na kasarnan.

Exit mobile version