Mutum 8,730 Sun Ci Gajiyar Aikin Ido Kyauta A Jihar Jigawa  

Aikin Ido

A ranar Larabar makon nan ne aka kammala gudanar da aikin gyaran ido da bada magani da gilashi kyauta wanda Kungiyar Matasa Musulmai ta Duniya, ‘World Assembly Of Muslim Youth’ (WAMY), da hadin gwiwar gwamnatin jihar Jigawa da gidauniyar Malam Inuwa, wanda aka gudanar ga al’ummar Jihar Jigawa a Asibitin garin Hadejia.

Jimillar mutane dubu takwas da dari bakwai da talatin, 8730, ne su ka ci gajiyar wannan tsari wanda aka shafe tsawon kwanaki hudu ana gudanarwa, 21-24 Nuwamba, 2021).

Jimillar Gilashin Ido da aka raba kyauta a cikin wadannan kwanaki (4) su ne guda 500, sai mutanen da aka rabawa magani kyauta a kwanaki hudu, su ne mutum dubu bakwai da dari biyar da casa’in da uku 7,593. Rana ta farko An ba wa mutane 450, ta biyu mutane 2,258, ta uku mutane 4,885. Har ila yau, mutanen da su ka amfana da samun aikin tiyatar ido kyauta a a kwanakin adadin su wadannanya kai 637.

Jim kadan da kammala shirin a wannan rana, sai kuma aka gudanar da dan kwarya-kwaryan taron yi wa juna barka da karrama jami’an lafiyar da su ka taka rawa cikin aikin ta hanyar raba musu Littafi mai tsarki, (Alkur’ani).

A jawabin da ya gabatar a ya yin rufewa da karramawar, shugaban kungiyar ta (WAMY) a Nijeriya, Dakta Isham Muhammad, ya bayyana matukar farin cikinsa da samun sa’ar farawa da kammala shirin cikin nasara, inda daga bisani ya bayyana godiya ga gwamnatin Jihar Jigawa da gidauniyar Malam Inuwa hadi da hukumar gudanarwa ta asibitin Hadejia, da fadar Sarki, inda daga karshe ya bayyana farin ciki da irin tarya da karamcin da ya samu a wannan Jiha.

 

Shi ma a nasa jawabin, Dakta Bihlali Abdallah, likitan da ya zo daga birnin Riyad na kasar Saudiyya, ya kuma gudanar da aikin tiyatar ido a cikin wannan shiri, ya bayyana cewa wannan shi ne zuwansa na biyu Nageriya, inda ya bayyana kasar a matsayin kasar da al’ummarta su ka san darajar baki wanda hakan na daga cikin dalilan da su ka kara masa karfin gwiwar dawowa kasar a wannan karo na biyu bayan da ya taba zuwa Jihar Katsina a wasu lokuta da su ka shude ya gudanar da irin wannan aikin agaji.

Haka zalika, Dakta Bihlali, ya kara da cewa abu na biyu da ya kara masa kaimi wajen sake zuwa Nijeriya shi ne yadda ya ga al’umma su na matukar bukatar aikin ido duba da yadda ya ga manyan mutane maza da mata su na turereniyar zuwa neman samun wannan aiki kyauta, inda ya kuma kara da cewar a kowane lokaci a shirye ya ke domin ya sake dawowa ya cigaba da wannan aikin jinkai ga ’yan Nijeriya.

Da ya ke gabatar da nasa tsokacin, Dakta Usman Muhammad, na sashen lafiyar ido a babbar Asibitin Hadejia, ya bayyana godiya, jinjina da yabo ga duka bangarorin da su ka hada karfi da karfe wajen gudanar da wannan aiki na agaji da taimako da jinkai ga al’umma.

Shi ma a cikin nasa jawabin, Dakta Usaini Muhammad Baban, shugaban gidauniyar Malam Inuwa, wacce mai girma shugaban hukumar bunkasa fasahar sadarwar zamani ta kasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), ya assasa ya ke kuma jibintar lamarinta, ya bayyana farin ciki da godiya ga dukkan masu ruwa da tsaki cikin wannan aikin alkhairi tare da fatan Allah Ya sakawa kowa da alkhairi.

Dumbin jama’a da su ka amfana da wannan aikin alkhairi da sauran al’umma duka, sun yi matukar godiya da farin ciki marar misaltuwa tare da fatan Allah Ya ba da ladan wannan aiki.

Kungiyar ta matasa musulmai ta duniya gabadaya, (WAMY), da gwamnatin Jihar Jigawa, karkashin jagorancin mai girma gwamna, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, (MON, MNI), da gidauniyar Malam Inuwa, da wanda ya assasa gidauniyar, mai girma shugaba hukumar bunKasa fasahar sadarwar zamani ta Kasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa, (CCIE) su na cigaba da samun yabo, jinjina, da addu’ar fatan alkhairi daga dumbin marasa lafiyar da su ka amfana da wannan tallafi da ma al’umma gabadaya a bisa wannan aikin taimako, agaji da kuma jin kai ga jama’a.

 

Exit mobile version