Abba Ibrahim Wada" />

Mutum Biyar Da Za Su Iya Maye Gurbin Wenger

Mutane biyar ne ake sa ran dayansu zai gaji mai koyar da yan wasan  Arsenal Arsenew Wenger dan kasar Faransa da zai ajiye aikinsa a matsayin mai horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal bayan da ya kwashe shekaru 22 yana jagorantar kungiyar ta Ingila.

Yanzu dai wannan labarin na can ya haifar da jita-jitar shin wai waye zai gaji Arsene Wenger ne, kuma yanzu haka an fara cece-ku-ce akan mutane 5 da ake zaton mai yuwa dai daga cikinsu ne zai gaji wannan Gadon da Wenger ya sauka.

Wadanda ake ta cece-ku-ce akansu dai su ne:

1 – Patrick Bieira dake kungiyar (New York City)

2 – Brendan Rodgers na kungiyar (Celtic)

3 – Joachim Loew  mai koyar da tawagar kasar (Jamus)

4 – Carlo Ancelotti (bashi da kungiya)

5 – Luis Enrikue (bashi da kungiya)

Kuma kowanne daga cikin wadannan mutanen da ake zaton ka iya samun damar dare mukamin na Manajan Arsenal, na da kyakkyawan tarihin nasarorin da suka samu a fagen tamola.

To sai dai babban jami’in gudanarwa na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Iban Gazidis ya ce hakika yana fuskantar babban kalubale na abinda ba zai yiwu ba, wato samun wanda zai maye gurnin Arsen Wenger.

Arsene Wenger dai ya bayyana shirin ajiye mukaminsa ne a kafar sadarwa ta zamani inda ya bayyana cewar bayan da ya tsaya da kyau ya lura da yadda al’amurra ke tafiya a rayuwarsa, ya kuma tattauna da jami’an kungiyar da yake yi wa aiki, sai ya yanke shawarar cewar lokaci ya yi da ya kamata ya ajiye hakanan ya huta, kuma ya nunawa kungiyar jin dadinsa da yadda suka bashi damar yi Arsenal aiki shekaru aru-aru.

To bayan bayyana shirin saukar tashi ne aka ce wasu ‘yan wasansa da suka hada da Tony Adams, da Thierry Henry suka bayyana yadda za su yi kewar Ogan nasu da suka bayyana a matsayin gwarzon tsara karatun tamola na Duniya.

 

Exit mobile version