Abba Ibrahim Wada" />

Mutum Biyu Ne Za Su Iya Lashe Firimiya

Mai koyar da tawagar ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana cewa kawo yanzu kungiyoyi biyu ne zasu iya lashe gasar firimiya ta bana ta wannan shekarar da ake bugawa.
Guardiola ya bayyana hakane bayan da kungiyarsa tasamu nasara akan kungiyar Westham United daci 1-0 a wasan sati na 28 da suka fafata a filin wasa na Ettihad dake birnin Manchester bayan Sergio Aguiro ya cilla kwallo daya tilo data basu nasara.
Sakamakon wasan yasa yanzu maki daya ne tsakanin Manchester City da Liverpool wadda take mataki na biyu sai dai tuni Tottenham ta fita daga jerin masu lashe gasar bayan da yanzu maki takwas na a tsakaninsu da Manchester City din.
“Yanzu saura wasanni 10 a kammala gasar nan kuma kowanne wasa idan aka samu nasara akwai maki uku saboda haka dole mu sake dagewa mu mayar da hankalinmu wajen ganin mun smau nasara akan abokan wasanmu” in ji Guardiola
Ya ci gaba da cewa “Tsakanin kungiyarsa da Liberpool ne dole za a samu kungiyar da zata lashe wannan gasar saboda Tottenham sunyi asarar maki shida cikin wasanni biyu da suka buga a baya bana nan saboda haka babu maganarsu yanzu”
Manchester City dai tana neman lashe kofin firimiya karo na biyu a jere yayinda Liberpool take fatan samun nasarar lashe gasar a karo na farko cikin shekaru 29 a duniya sai dai har yanzu akwai kalubale a gaban kowacce kungiya.

Exit mobile version