Mutum Shida Sun Mutu, Wasu Da Dama Sun Jikkata A Adamawa

An tabbatar da mutuwar wasu mutane shida da jikkata wasu da dama, biyo bayan fadar da ta kaure tsakanin Fulani makiyaya da jama’ar yankin Dumne dake karamar hukumar Song a jihar Adamawa.

Misis Doris Bashiru ita ce Kansila da ke wakiltar mazabar Dumne, ta ce lamarin ya fara kamar da wasa yanzu kuma gashi batun ya kaiga asaran rayukan jama’a da kone gidaje, ta ce bai kamata mutane su rika aika abu cikin fushi haka ba.

Ta ce lokacin da wani makiyayi yazo zai shayar da Shanu ruwa, sai ya same wani mutun na wanka, da shanun sukaji motsi a ruwa sai suka watse, shi ya sabbaba tashin rikicin.

Ta ce bayan da suka shiga tsakani maganar ta lafa, daga baya kuma rikicin ya sake barkewa lamarin da ya kaiga kashe mutum shida ciki har da wata tsohowa da ba ta da lafiya tana kwance aka cinna wuta a dakin da take.

“tsohowar dama ba ta da lafiya saboda haka bata iya gudu ba, to da yake wuta ake cinna ma gidaje, tana kwance a daki aka cinna ma dakin wuta, ta kone kurmus” inji Doris.

Rahotanni daga yankin na nuni da cewa rikicin ya kaiga kone garuruwan Tere, Sumba da kuma Cere duk a yankin mazabar Dirma dake karamar hukumar ta Song.

Tuni dai itama gwamnan jihar Umaru Bindow Jibrilla, cikin wata sanarwar manema labaru yayi Allawadai da faruwar lamarin, yace bai kamata a wannan lokacin da’ake kokarin samar da zaman lafiya da fahimtar juna, a samu tashin wani rikicin kuma ba.

Sanarwar wacce mai taimaka ma gwamnan kan harkokin sadarwa Macauley Hunohashi, ya aikewa manema labarai, ta jaddada matsayin gwamnan na cewa zai tabbatar doka ta yi aiki akan mutanen da ke haifar da fitina a jihar.

Sanarwar ta tabbatar da cewa hankali ya kwanta a yankin biyo bayan matakan kara yawan jami’an tsaron soji da ‘yan sanda, ta ce gwamnan na jajantawa jama’ar da abun ya shafa, sai kuma ta bukaci mutane da arika kai zuciya nesa.

To sai dai sanarwar ta alakanta yawaitar tashin-tashinan da ke kaiga salwantar rayukan da’ake samu da rashin tilasta mutane bin doka da oda da gwamnatocin da suka gaba basuyi ba, ta ce sai kowa ya bi doka ne za’a samu zaman lafiya.

“rashin tilasta bin doka da oda, ta sa mutane ke aikata irin wadannan kashe-kashen da wasu ayyukan barna, dole mu tabbatar anbi doka” inji Bindow.

Itama dai rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar tashin rikicin, sai ba ta yi wani karin bayani ba.

SP Othman Abubakar, shi ne kakakin rundunar a jihar, ya shawarci jama’a da cewa bai kamata suna daukan doka a hanu ba, “duk irin laifin da akayi maka ka sanar da jami’in tsaro su dauki matakin bi maka hakki, amma ba ka dauki matakin ramuwa ba” inji Othman.

Exit mobile version