Connect with us

MANYAN LABARAI

Mutum Tara Ne Suka Rasu Sakamakon Fashewar Tankar Gas A Garin Lafiya

Published

on

Adadin mutanen da suka rasa ransu a fashewar tankar gas da ya faru jiya litinin a garin Lafiya ta jihar Nasarawa ya kai tara, tankin ya fashe ne a wani gidan mai, mai suna “Monaco gas station” a garin Lafiya.

Gwamnan jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura yana cewa; jiya da dare mun samu labarin fashewar tankin gas, inda aka bada rahoton mutuwar mutum shida, amma zuwa yanzu da safe munji adadin mutanen ya kai tara, wannan abun alhini ne matuka, kuma zamu yi iya kokarin mu wajen taimakon wadanda suka samu raunuka daga fashewar.

‘Zuwa yanzu an samu an kai mutum 17 daga cikin 37 da suka samu muguwar kona, amma uku daga cikinsu rai ya yi halinsa a asibiti, yanzu akwai masu jinya mutum 14 kenan a wani asibiti na musamman a garin Abuja, zamu tabbatar da an baiwa masu konar kulawar da ta dace da su.’ Inji Al-Makura

Zuwa yanzu jami’an kashe gobara sun samu nasarar kashe wutar, suna kuma kokarin tabbatar da sun kautar da duk abinda ka iya jawo sake tashin wutar a wajen.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: