Mutum Tara Sun Rasa Ransu A Hatsarin Mota A Akan Hanyar Ibadan

Akalla mutum tara aka tabbatar da sun rasa ransu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a safiyar yau Talata, a kan babbar hanyar Ibadan zuwa Legas, wata babbar bas ce kirar Marcopolo ta yi taho mu gama da tarakta kirar Iveco, a daidai wani waje da aki kira Aseese.

Wani babban jami’an hukumar kiyaye hadura, yace hatsarin ya faru ne sakamakon gudu na fitar hankali da direban bas din mai lamba SMK 867 XG, inda matukin bas din ya kasa rike bas din, sai ya daki wannan tarakta din mai lamba AAA XP da misalin karfe 5:30 na safiyar yau.

Mutum 42 ne suke cikin bas din, maza 34, sai mata takwas, maza uku magidanta da mata biyu sun samu raunuka, mazan bakwai ne suka rasa ransu, sai kuma mata guda biyu, an garzaya da masu raunukan asibiti, sannan an ajiye jikunan wadanda suka rasa ransu a babban asibitin koyarwa wanda ke garin Sagamu.

Exit mobile version