Mutum Uku Sun Gurfana A Kotu Bisa Satar Awaki Da Kifaye

A makon da ta gabata ce, wasu mutum uku su ka gurfana a gaban kotun Abakaliki, bisa tuhumar su da satar awaki guda biyu da kifaye. Wadanda a ke tuhuma dai su ne, Mbam Oliber da Mbam Igabogu  da kuma Chukwuemeka Nwobu, ana dai tuhumar su ne da laifuka guda hudu wadanda su ka hada da na sata, shiga gidan mutane ba tare da izi ni ba, aikata babbar laifi da kuma hada kai domin aikata laifi. Bincike ya nuna cewa, su wadanda a ke tuhuma sun aikata wannan laifin ne tun a ranar 3 ga watan Nuwambar shekarar 2019, a yankin Igidiagbo da ke cikin karamar hukumar Abakaliki ta jihar. Wadanda a ke tuhuma dai sun afka gidan wani mutum mai suna Mista Godwin Nwogboga, sannan su ka sace masa awaki guda biyu. Haka kuma ana tuhumar su da shiga gidan wata mata mai suna Misis Cecilia Nwaji, inda su ka sace mata kifayenta.

Lauya mai gabatar da kara Barr Eze Ndubuaku, ya bayyana wa kotu cewa, laifin da su ka aikata dai yana da hukunci ne a sahe na 516A (a), 411 (A) da 390 na dokar manyen laifuka ta Jihart Ebonyi mai lamba kamar haka Cap 33 Bol. 1 ta shekarar 2009.

An dai karanta laifukan kamar haka, “kai Mbam Oliber da Mbam Igbogu da kuma Chukwuemeka Nwobu, a ranar 3 ga watan Nuwambar shekarar 2019, a yankin Igidiagbo Okpotumo da ke cikin karamar hukumar Abakaliki, kun hada kai a tsakanin ku sannan kuka aikata laifin sata, domin haka kun aikata laifi wanda ke da hukunci a sashen 516A (a) na dokar manyen laifuka ta Jihar Ebonyi mai lamba kamar haka Cap 33 Bol 1 ta shekarar 2009. “Kai Mbam Oliber da Mbam Igbogu da kuma Chukwuemeka Nwobu, a ranar 3 ga watan Nuwambar shekarar 2019, a yankin Igidiagbo Okpotumo da ke cikin gundunar Abakaliki, kun afka cikin gidan wani mutum mai suna Godwin Nwogboga da kuma gidan wata mata mai suna Cecilia Nwaji kuka yi musu sata, domin haka kun aikata laifi wanda ke da hukunci a sashe na 411(a) na dokar manyen laifuka ta Jihar Eboyi mai lamba kamar haka Cap 33 Bol 1 ta shekarar 2009. “Kai Mbam Oliber da Mbam Igbogu da kuma Chukwuemeka Nwobu, a wannan rana da lokaci cikin wannan gundumar, kun sace awaki guda biyu wadanda kudinsu ya kai na naira 65,000 da kuma kifaye wanda kudinsu ya kai na naira 15,000, mallakin wani mutum mai suna Godwin Nwogboga da kuma wata mata mai suna Cecilia Nwaji, domin haka kun aikata laifi wanda ke da hukunci a sashe na 390 na dokar manyen laifuka ta Jihar Ebonyi mai lamba kamar haka Cap 33, Bol 1 ta shekarar 2009.”

Sai dai ba a bayar da belin wadanda a ke tuhuma ba, sakamakon alkali mai shari’a Nnenna Onuoha ta bayyana cewa, wannan laifi ne da a ka aikata cikin dare wanda ya ke yi wa kotu wahalar warwarewa, sannan kuma ba a bayar da belin wadanda a ke tuhma nan take. Ta bayar da umurnin a karkame wadanda a ke tuhuma a gidan yarin Abakaliki tare da mika fayel din shari’ar ga ma’aikatar shari’a ta jihar domin samun karin shawarwari. Haka kuma ta dage wannan shari’ar har sai ranar 6 ga watan Junairun shekarar 2020.

Exit mobile version