Majiyar ayyukan jinkai a yankin arewa maso gabashin Nijeriya ta bayyana yadda matashiya yar kunar bakin-wake ta tayar da bam a cikin jama’a wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutum uku, ranar Asabar.
Ta bakin Abubakar Mohammed ya kara da cewa, “Mun kwashe gawawaki uku tare da karin wasu mutum biyu da su ka samu munanan raunuka a harin kunar bakin waken.”
Ya sanar da cewa, an kai wannan harin ne a garin Konduga, mai tazarar kilo mita 38 daga birnin Maiduguri ta jihar Borno.
Shima Ibrahim Liman, shugaban jami’an tsaron sa-kai a yankin ya shaidar da cewa, yar kunar bakin waken ta kutsa kai tare da tayar da bam din a cikin gungun wasu mutanen da ke harkokin su na yau da kullum kusa da fadar sarkin garin.
Ko a shekarar da ta gabata, an kai makamancin wannan harin, inda akalla mutum 30 su ka gamu da ajalinsu a garin Konduga, a sa’ilin da wasu yan kunar bakin wake guda uku su ka tayar da bama-baman da su ka dana a jikin su a lokacin da ake kallon wasannin kwallon kafa.