Al’ummar Sinawa wanda yawansu ya kai sama da biliyan 1 da miliyan 400 a halin yanzu, kasar na da yawan kabilu da suka kai 56 daga larduna da yankuna daban daban na kasar. Wani abin ban sha’awa shi ne, Sinawa mutane ne masu kokarin kiyaye al’adunsu wadanda aka gada daga kaka da kakanni. Wadannan al’adu sun hada da kiyaye tsarin zaman rayuwa, da nau’in tufafi, da tsarin abinci, da makamantansu.

Koda yake, da ma ance duk alummar da ta saki al’adunta zata iya wayar gari ta manta asalinta. Batun samar da abinci wani muhimmin ginshike ne da alummar Sinawa ke matukar baiwa muhimmanci domin wadata kasar da alummar kasar da abinci. A wannan hali da duniya ke fama da rashin tabbas, musamma duba da yanayin matsalolin da suka dabaibaye duniyar, misali, batun matsalar yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19, da karayar tattalin arzikin da duniya ke fuskanta, da matslolin sauyin yanayi, da bala’u daga indallahi dake neman jefa duniya cikin tsaka mai wuya kamar yadda hukumar samar da abinci ta MDD ta yi gargadi cewa akwai yiwuwar fuskantar matsalar karancin abinci a duniya. Koda yake, shekaru da dama da suka gabata, mahukuntan kasar Sin sun sha daukar matakai daban daban da nufin inganta fannin noma da samar da abinci ga kasar mai dunbun jama’a. Ranar 22 ga watan Satumba, rana ce ta bikin manoman kasar Sin, bisa ga alkaluma na baya bayan nan da hukumomin kasar suka fitar game da cigaban da aka samu a fannin noma sun nuna yadda aka noma karin hatsi a filayen noma a kakar girbi ta wannan shekarar da muke ciki. Hakan dai yana nuni da cewa Sin ta samu daidaito a fannin ayyukan gona, kana ta samu isasshiyar yabanya da tabbacin wadatar abinci. A lokuta da dama mahukunta kasar Sin sun sha nanata aniyar gwamnati na tallafawa manoman kasar ta hanyar samar da tsare tsaren inganta fasahohin noma, da samar da tallafi don raya wannan muhimmin fanni wanda sai da shi ne dan adam zai iya rayuwa a doron kasa. Ko a kwanan baya ma, sai da shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga daukacin al’ummomin kasar da su yi tsimin abinci, domin idan ba a samar da kuma adana isasshen abinci ba, to tilas ne a sayo daga kasashen ketare,

kuma mai yiwuwa ne a sayo shi da tsadar gaske. Har ma wasu masanan ilmin tattalin arziki sun taba yin kiran a gina masana’antu a dukkan gonakin dake kasar Sin don raya tattalin arzikin kasa, saboda a ganinsu, sayen abinci daga ketare zai iya damun alummar Sinawa. Tun a farkon wannan shekara, ake fuskanci kalubale da dama, ciki har da bullar cutar COVID-19, da ambaliyar ruwa mai tsanani a kogin Yangtze, wadanda suka haifar da kalubale ga fannin noma na kasar Sin. A mataki na kasa da kasa kuwa, annobar COVID-19, da yaduwar farin dango, da yawan rikice rikicen kungiyoyin masu dauke da makamai wadan ke kassara ayyukan noma sun sanya MDD yin hasashen yiwuwar fuskantar karancin abinci a wasu kasashen duniya a kalla 25 a wannan shekara da muke ciki. Game da hakan ne kuma, ake ganin cewa Sin ta yi namijin kokari wajen cimma nasarorin da ta samu ya zuwa yanzu, wanda kuma hakan zai iya yin tasiri ga samuwar isasshen abinci a duniya. Alkaluman kididdiga sun nuna cewa,

adadin abincin da al’ummun kasar Sin ke amfani da shi a shekara, ya kai kilogiram 470, wanda ya haura adadin da kasashen duniya suka cimma matsaya a kai wato kilogirma 400 ga ko wane mutum. Kazalika, yanayin wadatar abinci a kasar na kara kyautatuwa. Daya daga cikin muhimman dalilai da suka haifar da hakan kuwa shi ne, gwamnatin Sin tana dora muhimmancin gaske, ga batun samar da isasshen hatsi cikin dogon lokaci. A hannu guda kuma, Sin ta fitar da wasu muhimman tsare tsaren dabarunta, da kwarewar ta a fannin wanzar da wadatar abinci, tana kuma shiga a dama da ita a harkokin gudanarwa na samar da isasshen abinci a kasa da kasa. Bugu da kari, tana bayar da tallafin gaggawa na abinci gwargwadon iyawar ta. Matakin dake nuni ga irin kokarin da kasar ke yi wajen sauke nauyin da ke bisa wuyanta, a matsayin ta na babbar kasa a wannan fanni. Ko da a ranar 17 ga watan Satumbar wannan shekara, sai dai Sin ta samar da tallafin abinci na gaggawa ga kasar Sudan ta kudu.
Abinci shi ne ruhin rayuwar dukkan halittu, ba a iya rayuwa tilas sai da abinci. Wannan ne dalilin ne ya sa mahukunta kasar Sin ke kara azama wajen tabbatar da wadatar al’ummar kasar da abinci. A cikin shekaru 71 da suka gabata tun bayan kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin, kasar ta samu manyan nasarori a fannin wadatar abinci lamarin da ya baiwa duniya mamaki duba da yawan jama’ar kasar wanda a bisa kiyasi ya nuna adadin Sinawa ya zarta biliyan 1 da miliyan 400. Wannan kokari ya taimaka matuka lamarin da ya sa kasar Sin ta bayar da babbar gudunmawar kawar da yunwa a duniya, kamar yadda shugaban hukumar adana hatsi da kayayyakin amfanin gona na kasar Sin Zhang Wufeng, ya taba bayyana cewa, tun daga shekarar 1949 har zuwa yanzu, a koda yaushe, Sin tana sanya batun magance yunwa a gaban dukkan ayyukan tafiyar da harkokin kasar. Sai dai abin mamaki baya karewa duk da wannan namijin da kasar ke yi lamarin ya tsolewa wasu kasashen yamma ido har ma sunanuna fargaba kan batun wato ko kasar Sin za ta iya renon al’ummarta da kanta a daidai lokacin da duniya ta karkata kan batun yaki da bullar cutar numfashi ta COVID-19 a duk fadin duniya. To amma abin ban sha’awar shine alummar Sinawa mai kabilu sama da 56 suna cigaba da tsayawa tsayin daka wajen amsa kiran hukumomin kasar na bunakasa dadaddiyar sana’ar noma wanda masu hikimar Magana ke yi take da “Na duke tsohon ciniki kowa ya zo duniya kai ya tarar”. A karkashin jagorancin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kasar ta cimma nasarar samar da isasshen abinci bisa namijin kokarin da take yi. Batun samar wa Sinawa isashen abinci yana daga cikin manyan ajandojin jam’iyyar JKS mai mulki a kullum. A watan Satumbar da ya gabata, babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya ba da wani muhimmin umarni na a daina barnata abinci, inda ya yi nuni da cewa, kowa ya sani cewa duk wata kwayar abinci da wahalar aiki ne ake iya samunta. Ko da yake, a wannan shekara tasirin cutar numfashi ta COVID-19 da ta addabi duniya tana kuma kawo illa ga tattalin arzikin kasar Sin, amma kasar Sin za ta iya samar da isashen abinci ga al’ummarta. Alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar game da yawan kayayyakin gona, musamman shinkafa da kasar za ta samu a wannan shekarar ta 2020 ta nuna cewa, yawan shinkafar da aka samu a kasar a kashin farko a 2020, ya kai ton miliyan 27.29 inda ya karu da ton miliyan 1.08, wato ya karu da kashi 3.9% idan an kwatanta da makamancin lokacin shekatar 2019. Shi ma Ke Bingsheng, tsohon shugaban jami’ar aikin gona ta kasar Sin ya ce, kasar Sin ta samu manyan nasarori ta fuskar wadata kasar da abinci idan an kwatanta da farkon lokacin aiwatar da manufar yin sauye-sauye a gida da bude kofa ga ketare. Huang Jikun, direktan cibiyar nazarin manufofin aikin gona ta kasar Sin ta jami’ar Peking, ya bayyana a yayin da yake ganawa da wakilin jaridar The China Science Daily cewar, tsananin kalubale da kasar Sin take fuskanta yanzu shi ne a cikin shekaru 2 ko uku masu zuwa, ko kasar Sin za ta iya rage yawan alkama da shinkafa da ta adana a dakunan adana hatsi. Yanzu yawan hatsin da kowane Basine ya samu ya kai kilogram 474 maimakon kilogram 400 da ya kamata kowane mutum a duniya ya dace ya samu a duk shekara. Kuma yanzu kasar Sin ta kan shigar da wasu kayayyakin gona miliyoyin ton domin renon dabbobin gida kawai. Sabo da haka, ya kamata wadanda suke nuna damuwa kan wannan batun su kwantar da hankulansu, domin Sinawa suna iya renon kansu da abincin da suke samarwa da kansu. Ko shakka babu, halayyar Sinawa na rungumar al’adun noma da amsa kiran shugabanninsu dangane da irin kiraye kirayen da suke na karfafa aikin noma da samar da abinci ga kasa yayi matukar taimakawa alummar kasar wajen samun tagomashin abinci ga kasar mai yawan al’umma, har ma ya taimakawa kasa da kasa daga dukkan fannoni. Masu hikimar magana na cewa, “himma ba ta rago bane”. (Ahmad Fagam, CRI Hausa)