Abdullahi Muhammad Sheka" />

Mutuwar Abba Kyari Babban Rashi Ne Ga Wannan kasa – Alhassan Rurum

Shugaban Wakilan Majalisar Tarayya ta kasa, na shiyyar Arewa Maso Yamma kuma Wakilin kananan Hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure, Alhaji Kabiru Alhassan Rurum ya bayyana rashin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban kasa, Malam Abba Kyari a matsayin wani babban rashi ga kasar nan.

Jawabin haka, na kunshe ne cikin sakonsa na ta’aziyya ga Shugaban kasa Muhammad Buhari, tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ya yi fatan Allah (SWT) Ya kyautata makwancin Marigayin, Ya kuma baiwa Shugaban kasa da iyalai da ‘yan’uwan na Abba Kyari hakurin jure rashinsa da aka yi.
Haka kuma, Rurum na amfani da wannan dama wajen mika sakon ta’aziyyarsa ga mai martaba Sarkin Rano, Ambasada Dakta Tafida Abubakar 11, da Masarautar ta Rano, bisa rashin dan’uwa ga Sarkin Alhaji Ali Ma’aji Rano, wanda ya rasu bayan ya sha fama da doguwar jinya.
Hon. Rurum, ya bayyana Marigayi Alhaji Ali Ma’aji a matsayin mutumin da ya taimakawa al’umma a lokacin da yake raye. Sannan ya yi addu’ar Allah Ya ji kan sa, Ya kuma sa Aljanna ta zama makoma a gare shi.
A karshe kuma, Shugaban Kwamitin Fanshon na Majalisar Wakilan kasar nan, ya yi addu’ar Allah Ya baiwa Sarkin na Rano da iyalai da sauran daukacin al’ummar kananan Hukumomin Rano, Bunkure da Kibiya, hakurin jure wannan rashi.

Exit mobile version