Tare Da Bilkisu Yusif Ali – 08054137080– bilkisuyusuf64@gmail.com
A yau al’ummarmu suna cikin wani tarnaki na mutuwar aure inda kowanne bangare ke kuka da abokin zamansa akan cewar shi ne silar mutuwar aure.Masu karatu sun turo da dalilansu da suke gani su suka janyo mutuwar aure.
Sarra Tasi’u Ya’u
Babban dalilin da ke janyo mutuwar aure shi ne da ma samarin da ke zuwa neman aure a ba su bas u shirya ba ko kuma in sun ma shirya din to ba su san yadda ake daukar nauyin ci da sha da sutura ba da an zo an zauna sais u fara gajiya su ji auren ya gundure su .To fa daga nan sais u fara jin haushin matar kome ta yi musu sai su ji kamar ta watsa musu wuta daga nan sai saki ya biyo baya.
Aisha Shehu Maimota
Rashin hakuri da sanin menene hakkin aure a shari’ance shi ya janyo tabarbarewar zamantakewar aure a yau.Duk bangarorin biyu suna da laifi a dalilin mutuwar aure don kuwa karfedaya bay a amo.Tun kafin aure ya amata ma’aurata su san dole ne hakuri a zamantakewar aure.Abin da iyayenmu da kakanninu ke fada na a ji a ki ji a gani a ki gani tabbas haka yake.Hakurin nan fa na kowanne bangare ne ba wai namiji shi kadai ba ko kuma macen.Sannan me addinin muslunci ya fada kan auren.Ma’aurata ya kamata su san aure ibada ne don haka kome da ke cikin auren yana nan cikin addini to sanin me addinin ya fada shi ma wani mataki ne na rage mace-macen aure.
Mubin Ali
Rashin Biyayya musamman a wajen matan yanzu da rashin iya tafiyar da mazajen shi ya janyo auren ba ya yin nisa.Yarinya kafin ta zo a waje tana ta kaffa-kaffa ba ta son abinda zai bata ma rai ko kara ka gindaya ba za ra ketara ba amma da zarar an yi auren daga nan za ta mike kafa bukatarta ta biya ta shigo sai ta fara yi ma mijin gani-gani shi kuma miji sai ya ga ai shi ne shugaba a haka a haka in many aba su shiga maganar ba sai abu ya lalaace saki ya biyo baya.
Bara’atu Maikadara
Iyaye suna taka muhimmiyar rawa wajen zama silar mutuwar auren ‘ya’yansu.Iyaye musamman uwa it ace makarantar farko ta ‘ya’yayensu.Duk yanda uwa take yi a gidanta haka ‘yarta za ta dauka ta tafi da shi gidan mijinta.Idan uwa mai tsafta ce to tabbas ‘yarta za ta koyi tsaftar haka idan mai hakuri ce ko kuma mafadaciya ce marar tarbiyya marar biyayya ga miji duk tana koya wa ‘ya’yanta.Idan uwa ta dora yaranta kan bakin kishi kullum suna fafatawa da abokiyar zamanta to fa ita ma ‘yarta haka za yta taso bag a maciji da abokiyar zama.Don haka iyaye musamman mata su dage sub a wa yaransu tarbiyya su koya musu ayyukan gida kamar girki da tsafta.Sannan suke nusar da yaransu lokaci zuwa lokaci kan zamantakewar aure .
Asama’u R Ali
Talauci shi ne babbar matsalar da take kasha aure a yau da zarar kayan gara sun kare to fa zaman lafiya ya fara tangal-tangalMaza ba sa son ba-ni-ba-ni sannan ba za su iya daukar dawainiyar auren ba don haka da mace ta ishe su da bukatu sai su ya da dan mangwaro su huta da kuda.
Kabiru Mukhtar
Aure ne ake dora shi akan karya a tsakanin dukkan bangarorin.Namiji zai zo ya yi ta yi wa mace karyar arziki watakil ma arowa ya yi motar da yake hawa da kayan da yake sawa hatta kudin da yake yi wa budurwar burga duk na rance ne ko rigima ce ita kuma kwadayi sai ya rufe matai do ba za ta tsaya ta fuskanci gaskiya ba.Wasu ma ana tsaka da wannan wani na mutunci zai zo ta kore shi ko kuma da ma yana nan amma ganin wancen dan karyar sai ta kore shi a zatonta wannan ne za ta hut aba za ta Ankara ba sai an yi auren.Wani namijin hatta laife na aro ne ni nag a wanda da aka kawo laife y ace kada a dinka kayan sai bayan biki zai kai mata dinki Dubai don haka aka yard aba a taba kayan ba ashe na haya ne tana tarewa ya jide kayan tsaf ya mayar da su inda ya karbo wannan ne dalilin mutuwar auren.
Asama’u Sani
Rashin bincike yayin aure shi ne kusan dukkan silar mutuwar aure a yau.Dukkan bangaren biyu gidan mata da a maza an watsar da abinda shari’a ta yi umarni da shin a yin bincike namiji ya samarwa ‘ya’yansa uwa ta gari haka ita ma ta samawa ‘ya’yanta uba na gari hakan kuwa ba zai tabbata ba sai iyaye sun tsananta bicike lokacin da suka tashi auren ‘ya’yansu.A yau iyaye musamman na bangaren mace idan aka zo neman auren ‘yarsu in dai mai hannu da shuni ne ta fa ba bincike ko da kuwa an sami wani da ya san wani abu mummuna a bangaren mai neman ‘yar tasu sai su nuna bakin ciki ne.
Tukur Jikamshi
Rashin hakuri da godiyar Allah da wasu matan ke yi shi yake kawo mutuwar aure a yau.Namiji zai yi ta kokari amma daga ranar da suka nema babu to fa ba zaman lafiya hatta ma abin kirkin da aka yi a baya sai ya zamana sun rintse ido sun yi rashin kirki.Kowa kuma yasan yadda rayuwa take a yau yin wannan sai namiji in bai kai zuciyarsa nesa ba sai ya aikata abinda ba a so wato saki.
Big Boy
A yau kawaye ke kashewa mata aure musamman matan yanzu.Wata matar kawaye ke juyata su ne abokanan shawararta duk wani abu na tsakaninta da mijinta a bakin kawaye.To in aka yi rashin sa’a kawayen ba na kirki ne ba sai su dorata a hanya marar kyau kuma da ma sub a auren suka yi ba a karshe sai auren ya lalace.A wani lokacinma kawar ce za ta lallabo ta aure mijin bayan ta zuga kawar tata ta bar gidan.
Hafsy
Iyayen miji da dangin miji a yau suna taka muhimmiyar rawa wajen mutuwar auren dansu ko dan’uwansu.Da iyayen miji za su daina sa ido ‘yan’uwan miji su daina Gadara a giidan dan’uwansu da an zauna lafiyA
Nan za mu tsaya sai wani satin in mai duka ya kai mu za mu zo da namu bayanin kan Alhakin wa ye.Wadanda ba su ga sakonsu ba su yi hakuri ya zama maimaici ne ko kuma ya zo a makare.