Mutuwar Dan Kwallo: An Fafata A Tsakanin ‘Yan Sanda Da Masu Zanga-zanga A Shagamu

Akalla mutane biyar ne da suka hada da ‘Yan sanda biyu aka kashe ranar Litinin a lokacin da daruruwan masu zanga-zanga suka kwarara a bisa titunan garin Shagamu, ta Jihar Ogun, inda suke nuna bacin ransu a bisa mutuwar wani dan kwallon kafa mai suna, Kazeem Tiamiyu.

Tiamiyu, wanda dan wasa ne a kungiyar kwallon kafa ta Remo Star Football Club, an kashe shi ne a ranar Asabar lokacin da wani dan sanda ya kama shi a bisa tuhumar cewa shi dan dandatsan nan ne a yanar gizo na Yahoo Boys.

Rahotanni sun nuna cewa wata mota ce wacce take tafe a guje ta banke Tiamiyu, a lokacin da ‘yan sandan suke tafiya da shi ofishinsu a Abeokuta, a lokacin da motar ‘yan sanda ta lalace a kan hanya ana ta faman gyaranta.

Mutuwar na shi ta fusata al’umman garin na Shagamu, inda suka dauka cewa ‘yan sanda suna kokarin tsame jami’ansu ne a bisa sanadiyyar mutuwar na shi.

Al’ummar gari sun fara zanga-zanga a ranar Litinin da safe, dauke da kwalaye da ganyayyaki, inda su ke kewaye titunan garin na Shagamu.

Zanga-zangar ta ranar Litinin ta baci ne a lokacin da aka turo ‘Yan sanda domin su kwantar da lamarin, inda kuma a ka zargi ‘yan sandan da fara yin harbi a kan masu zanga-zangar.

Rahotanni sun nuna cewa, harsashi ya sami mutane uku cikin masu zanga-zangar inda kuma aka yi zargin duk sun mutu a nan take, sa’ilin da mutum na uku ya rasu a bayan an kai shi Asibiti.

An ce hakan ne ya sanya taron jama’ar suka far ma ‘yan sandan, aka kuma yi zargin cewa sun kashe biyu daga cikin ‘Yan sandan a matakin daukan fansa, daga nan kuma mutanan suka shiga kona tayoyi a kan titunan garin.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar, (CP) Kenneth Ebrimson, ya musanta cewa ‘yan sandan sun budewa masu zanga-zangar wuta.

Kwamishinan ya ce, “Sam ba mu harba ko harsashi guda ba. Ina garin na Shagamu a maganar nan da nake yi da ku. Ai mun rigaya mun baiwa masu zanga-zangar hakuri har duk sun koma gida. A cikin lumana. Abin da ya faru shi ne, wasu zauna gari banza ne suka so yin amfani da wannan damar domin su haifar da tashin –tashina a Jihar.

“Su ne suka yi kokarin cinna wa ofishin ‘yan sandan wuta, amma sai ‘yan sanda suka watsa su. Amma sam ba mu harba ko harsashi guda ba a kan masu zanga-zangar duk da tsokanar da suka yi ma na.

“Mun dauki duk matakin da ya kamata mu dauka a kan lamarin. Mun biya wa masu zanga-zangar bukatunsu, mun kuma tabbatar da an kama tawagar ‘yan sandan da suka kama dan was an kwallon, a yanzun haka ma suna nan a tsare suna fuskantar ladabtarwa.”

Mataimakin babban sufeton ‘yan sanda mai kula da shiyyar Zone II da ta hada da Jihohin Lagos da Ogun, Ahmed Iliyasu, ya yi tir da faruwar lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ta Tiamiyu, sannan ya gargadi jami’an ‘yan sanda da cewa duk wanda aka kama da saba dokar aiki zai fuskanci hukunci kamar yanda doka ta tanada.

Exit mobile version