Musa Muhammad" />

Mutuwar Masana’antu Da Matsalolin Tsaro A Kasar Nan

Mai karatu a yau ma Allah cikin ikonsa ya kawo mu wani makon, inda muke ci gaba da yin bayanai game da abubuwan da suka shafi rayuwar mu ta yau da kullum, musamman wadanda suka shafi mafiyawa daga cikin al’umma, wato matasa, domin matasa su ne ginshikin ci gaban kowace al’umma, kuma idan aka yi duba za a ga cewa wadannan matasa su ne kashi kusan 70-80 cikin 100 na al’umma. Don haka kula da ci gaban su, shi ne ci gaban al’umma.

Na sha fadin cewa matasa ne kashin bayan kowane irin ci gaba a tsakanin al’umma ko akasin ci gaban, wanda hakan ta sa a kowane rubutu nawa nake yawan yin tsokaci a kansu, wajen jawo hankulansu da su kasance masu halaye nagari, tare da yin kira ga Hukumomi da masu ruwa da tsaki su taimaka wajen kula da matasan.

A yau ina so ne in yi dan tsokaci ne game da wani muhimmin abu, wanda jama’a da dama ke ganin gwamnatoci da masu hannu da shuni sun yi sake da su. Wannan ba wani abu ba ne illa yadda aka masana’antu, masakun mu da sauran manyan kamfanoni suka mutu murus, musamman a wannan yanki na Arewacin kasar nan, wanda kuma mutuwar wadannan wutare ba karamin illa ba ne gare mu.

Na ce ba karamin illa ba ne gare mu bisa la’akari da cewa wadannan wurare suna sama wa al’ummarmu, musamman matasanmu da dama ayyukan yi, wanda samun wadannan guraben ayyuka suna matukar taimakawa wajen rage munanan ayyuka ga matasa, wanda kuma rashin sa ke jefa da dama daga cikinsu wajen shiga munanan ayyuka.

Wadannan masaku da kamfanoni, a lokacin da suke aiki ba a samun irin fitintinun da ake samu a yanzu, ba a samun yawan bata garin da suke da yawa a tsakanin jama’a kamar yada suke a yanzu, ba a samun yawan zauna-gari banza irin wadanda muke da su a halin yanzu.

Ga duk masu bibiyar abubuwan da ke tafiya na yau da kullum za su iya ganin irin illar da wannan abu ya kawo wa al’umma a wannan zamani. Domin a lokacin da wadannan wurare ke aiki, abin zai ba ka sha’awa ka ga yadda jama’a ke tururuwa wajen zuwa da kuma dawo aiki, jama’a da dama na cin abinci, baya ga masu daukan albashi, akwai kuma masu jigila da saye da sayarwa a wadannan wurare. Babu wanda zai iya tantance yawan jama’ar da ke gudanar harkokinsu na samun taro-sisi a irin wadannan wurare.

A kodayaushe idan aka yi magana game da mutuwar wadannan wurare, jama’a da dama suna dora alhakin abin a kan wiyar gwamnatoci, tun daga na tarayya, jihohi har zuwa Kananan Hukumomi na ganin cewa hakkinsu ne kula da wadannan wurare.

Lallai haka ne, Hukumomi ne ke sahun gaba wajen daukar laifi, domin su ne suke da karfin iko da arzikin da za su iya yin hubbasa wajen dawo da martabar wadannan wurare. Wannan ma ya sa masu neman mukamai da a wadannan matakan mulki idan suna neman a zabe su, su kan yi alkawuran cewa za su dawo da martabar wadannan wurare muddin aka zabe su, amma abin takaicin, har yanzu babu wani zababben da ya yi wani yunkuri na yin hakan.

Kullum idan ana magana kan irin wannan masaku da kamfanoni da suka ruguje, babu inda takaici zai kama mutum sai in ya yi waiwaye zuwa Kaduna da Kano, inda a wancan lokacin duk wadannan garuruwa akwai Unguwanni, musamman da iri wadannan masaku ne suka ja  masu suna. Misali a Kaduna a ce Kakuri/Makera. A Kano kam wuraren suna da yawa.

Wani abin dubawa, lallai kamar yadda na fada a sama, za a iya cewa duk wadannan abubuwa laifin gwamnatoci ne, amma ba su kadai ba, masu kudinmu ma suna da babban laifi. Domin ai ko a masaku da kamfanonin da muka yi magana wadanda suka durkushe, yawanci na ‘ya kasuwa ne, ba gwamnatoci ne kadai ke da su ba, me zai hana su ma su sake zuba jari don farfado da su?

Domin ana yawan maganar cewa ba za a iya bar wa gwamnatin komai a ce sai ita ce za ta yi ba, musamman a wannan zamani da muke da yawan da ya wuce misali.  Domin a halin yanzu an ce a Nijeriya muna kusan mutum Miliyan 200 ne. Don haka lallai wajibi ne masu kudinmu su shigo ciki don ceto matasan nan namu daga halin da suke ciki na rashin aikin yi.

Rashin tsaron da muke fama da shi yanzu a kasar nan, musamman a nan Arewa yana tsoratar da masu zuba jari daga kasashen wajen su zo don kafa masana’antu, duk da yake wasu Gwamnoni suna kokarin wayar da kan irin wadannan ’yan kasashen wajen cewa abin bai kai yadda suke gani a kafafen yada labarai ba, inda kuma wasu ke zuwa suna dubawa. Musamman a Kaduna, Malam Nasiru El-rufai yana kokarin gudanar da wadannan abubuwa.

To, amma duk da haka, ina ganain ai sai mu ’yan kasa mun yi wani hobbasa, gwamnatocinmu da masu kudinmu mun kafa irin wadannan masana’antu, sannan su wadannan ’yan kasashen wajen sun ga alama da gaske ne kafin har su ma su saki jiki su zo su kafa.

Na takarkare ina ta yin wannan bayani game da muhimmancin farfado da irin wadannan masana’antu ne bi sa la’akari da cewa mutuwarsu ne ummul haba’isin kusan duk fitintinu da rugingimun da suke addabar mu a wannan yanki namu da kasar baki daya. Na fi mayar da hankali a Arewa ne domin su ’yan Kudanci abin nasu da sauki, don har yanzu akwai masana’antun da ke aiki a wurinsu.

Shi matashi, idan yau ya wayi gari ya ga akwai inda zai je ya samu taro-sisi, musamman wadanda ba sa zuwa makaranta, to ba yadda za a yi a yi amfani da shi wajen aikata wani mummunan abu. Amma idan aka wayi yau matashi ba inda zai je, to zai iya shiga kowane irin hali don samun abin da zai biya bukata, ko da kuwa ta mummunar hanya ce.

Wannan ne ya sa muke da tunanin cewa rugujewar wadannan masana’antu da kamfanoni ya taimaka matuka wajen jefa kasar nan cikin mummunan halin da take ciki na rashin tsaro, bisa la’akari da yawan matasan da ba su da inda za su je don neman abin da za su ci.

Saboda haka yana da matuwar muhimmanci gwamnatoci da masu hannu da shuni su zo su sake duba batun farfado da wadannan wurare don amfanin al’ummarsu, su samu riba, sannan kuma jama’a su samu aikin yi da zai taimaka masu wajen magance matsalolin su na yau da kullum.

Sannan kuma yin haka zai zama ya kawo wa sauran al’ummar kasa sauki wajen rage masu aikata mumaman ayyuka don samun zaman lafiya da ci gaban al’umma da ci gaban arziki.

A biyo mu mako na gaba in Allah Allahu.

Exit mobile version