Hussaini Baba" />

Mutuwar Shugaban APC Da Garkuwa Da Mutane Ba Su Hana Zabe A Zamfara Ba

Babban zaben kasa ya gudana a jihar Zamfara duk kasancewar shugaban jam’iyyar APC na ‘Yandoto da ke cikin karamar hukumar Tsafe, Alhaji Yusuf Agege, ya rasu a daren Juma’a sakamakon hadarin mota da ya yi daga Tsafe zuwa ‘Yandoto tare da abokin tafiyarsa, Bala Yusif. Haka nan kuma zaben bai samu tsaiko ba duk da a yankin Wanzamai masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutane a garin.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara ta tabbatar da cewa, shugaaban jam’iyyar APC da abokin tafiyarsa sun rasu ne sakamakon hadarin mota kuma ba a samu ko Kwabo a matarsa ba, sabanin yadda a ka rika yadawa da fari.
Jama’a dai na cewa, shugaban jam’iyyar ya amshi kudin da za a raba wa ejant da mutane lokacin zabe daga Tsafe, inda wajen tahowa gida ya gamu da ajalinsa.
Sai dai kuma a yayin zagayen da wakilinmu ya gano cewa, mutane ba su fito ba kamar zabukan baya kuma su ma malaman zabe ba su kai kayan zabe a kan lokaci ba, kamar yadda a ka sanar. Wannan ya sanya wasu koma wa gidajensu kuma ba su kada kuri’a ba.

Exit mobile version