Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAUSAYIN MUSULUNCI

Mu’ujizozin Annabi Isah (AS) Da Aka Bai Wa Annabi (SAW) Har Da Kari (I)

by Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani
December 18, 2020
in DAUSAYIN MUSULUNCI
4 min read
Mu’ujizozin Annabi Isah (AS) Da Aka Bai Wa Annabi (SAW) Har Da Kari (I)
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Mu’ujizozin Annabi Isah (AS) Da Aka Bai Wa Annabi (SAW) Har Da kari (I)
Amma game da abin da Allah ya bawa Annabi Isah (AS), cewa yana raya makafi da warkar da kutare da raya matattu, an bawa Manzon Allah (SAW) shi ma. Manzon Allah ya mayar da idon katadatu da aka cire masa a wurin yaki. Lokacin da aka cire wa katadatu idon sai ya dauko ya kawo wa Manzon Allah ya mayar masa. katadatu ya ce idon da Manzon Allah ya mayar masa ya fi gani da shi a kan dayan. Kuma Manzon Allah ya yi tofi a idon Sayyidina Ali (RA) ranar yakin Khaibara lokacin yana ciwon ido (apolo), sai ga idon ya washe ya yi fari ya warke. Kuma zancen albaras ma (ciwon kuturta) matar Mu’azu bin Afra’a kuturta ta fito mata, Manzon Allah (SAW) ya yi mata addu’a, ya sa sanda ya taba wurin ciwon matar ta warke.
Game da raya matacce kuma, a cikin littafin Baihaki na Dala’ilun Nubuwwah, akwai kissar mutumin da ya ce da Manzon Allah (SAW) “ni ba zan yi imani da kai ba sai ka raya mun ‘yata (da ta mutu), sai Manzon Allah ya je kabarinta ya ce “ya wance (ya ambaci sunanta)” sai ta amsa wa Manzon Allah (SAW). Sai Manzon Allah ya ce “ga babanki ya ce ba zai yi imani ba sai na tayar masa da ke, amma me kika gani?” sai ta ce “a’a, ya Rasulallahi abin da yake wurin Allah ya fi abin da yake wajen babana”. Baban ya sa kuka ya ce “na bar ki da Ubangijinki, ya Rasulallahi kyale ta, na yi imani”. Ka ga a nan Manzon Allah ya raya matacce.
Ba ma matacce dan Adam da ya taba zama mai rai ba, Manzon Allah (SAW) ya taba raya abin ma da ba shi da rai tun asali, wannan kuma ya fi ban mamaki. Tsakwankwani sun yi tasbihi a hannunsa (SAW). Kututturen dabino ya yi bege saboda Manzon Allah ya bar shi, har ma ya yi kuka kuma duk sahabbai har da wadanda suke wajen masallaci duk sun ji kukan. Kututturen ya yi kuka ne yana iccensa ba sai da ya zama wani abu ba daban. Wasu abubuwa ba domin Annabi ne ya yi ba, wasu za su iya cewa damfara ce. Ka ga dai icce yana kuka, ai abin ya fi karfin hankali. Shi mumini idan ya ga haka zai ce daga Allah ne, shi kuwa munafiki zai ce ai tsafi ne. Kuma irin wadannan abubuwa na mamaki ba ma Manzon Allah (SAW) ba kansa, a cikin manyan bayin Allah na al’ummarsa ana samun masu irin wannan karama. Mumini zai yi imani amma munafiki zai karyata.
A samu kututturen dabino ya bude baki ya yi magana shi ya fi kai isa matuka a kan mutum matacce. Domin shi kututture yana daga cikin jinsin abubuwan da ba su yin magana.
Amma abin da Allah ya ba Annabi Isah (AS) na daga ilimin sanin duk abin da mutane suka boye a cikin gidaddajinsu, da abin da suka ci, shi ma Annabi (SAW) an ba shi har da kari. Annabi Isah yakan ba mutanensa labarin abin da suka boye suka ci a gidaddajinsu, wannan mu’ujiza ce. To, shi kuwa Manzon Allah (SAW) Allah ya ba shi fiye da wannan, ba kawai abin da aka ci a gida ko aka boye ba, duk wani abu da ke boye Allah ya ba Manzon Allah ilimin saninsa. Manzon Allah ya ce an ba shi makullan duk wani abu na boye. Wata ruwaya kuma ta ce “an ba wa Annabinku sanin komai”. Mutum ya je ya dau littafin “Hujjatullahi Alal Alamiyn” na Nabahani zai ga abubuwan da ya wuce hankali ko ya dau Muktari’atul Asliyya da yake magana a kan ‘Technology’ na zamanin nan, duk wani abu da aka fitar da shi na kimiyya da fasaha sai da mai littafin ya kawo Hadisi a kan abin, ma’ana duk wani abu da aka gani na kimiyya sai da Manzon Allah (SAW) ya fade shi.
Imamu Suyudi da Askalani da Imamu kasdalani da Zarkani da Sawi a bisa Jalalaini sun tafi dukkansu a kan cewa dukkan gaibukan nan guda 5 Allah ya sanar da Manzon Allah (SAW).
Allah shi kadai ilimin kiyama yake wajensa, to kuma sai wanda ya ga dama ya sanar da Manzon Allah (SAW). Idan mutum bai sani ba, to ga malamai magabata da suka tafi a kan haka, in dai mutum gaskiya yake nema sai ya ajiye jahilcinsa ya dauki na malaman. Malamai magada Annabawa ne, abin da Annabawa suka zo da shi suke fassarawa. To wadannan malamai sun ce Allah ya ba wa Annabi (SAW) ilimin gaibukan nan guda 5. Ya san kiyama amma dai ba a yi masa izinin ya fada ba. A lokacin da Mala’ika Jibrilu (AS) ya tambaye shi yaushe ne za a yi tashin kiyama? Amsar da ya ba wa Jibrilu ita ce “Wanda ake tambaya bai fi mai tambaya sani ba”. Ka ga yanzu Jibrilu kansa ya sani. To Allah zai iya sanar da Jibrilu amma bai sanar da Muhammadur Rasulullahi (SAW) ba? Ka ga ba zai yiwu ba.
Amma Jibrilu ya yi abin da muke cewa “gwari-gwari (bayani dalla-dalla)”. Sai ya tambayi Manzon Allah (SAW) cewa, to ba ni labarin alamomin kiyama. Yanzu wanda bai san abu ba za a iya tambayarsa ya kawo alamomi? Kuma a cikin Hadisin Manzon Allah (SAW) bai ce ai alamomin ma bai san su ba. Sai ya dinga fada… kuma duk wani abu da za a yi kafin kiyama sai da Manzon Allah ya fada.
Allah shi ya san yaushe ruwan sama yake sauka kuma ya sanar da Manzon Allah. Yanzu ma a wannan zamanin ga technology nan ya zo; sai ka ga kafura mai shiga ta rashin kamala ma tana fadar wannan ilimin da wuraren da za a yi ruwa a duniya. Yanzu ya kenan? Mai musu dai ba zai karyata Allah ba da ya ce shi kadai ya san saukar ruwan sama. Illa abin da zai iya cewa shi ne, Allah ne ya kawo wani abu na kimiyya ya sanar da kafuran nan ilimin abin. To, ko haka a gaya wa Annabi (SAW) a ce Allah ne ya sanar da shi mana, amma ba musu ba. Manzon yakan yi addu’a ba hadari kuma a saukar da ruwan sama. Ya taba cewa, Mala’ikan Ruwa ya fada masa zai je ya yi ruwa a Yemen.
Za mu tashi a ci gaba da bayani kan wadannan gaibuka guda biyar da Allah ya sanar da Annabi (SAW) a mako mai zuwa cikin yardar Allah.
Sallallahu alal fatihil khatimil hadi wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil azim.

SendShareTweetShare
Previous Post

Bude Iyakokin Tudu: NIS Ta Yi Gargadi Game Da Bin Dokokin Shige Da Fice

Next Post

Matsalar Bushewar Gaba Da Maganinta

RelatedPosts

Darajojin

Darajojin Manzon Allah (SAW) Da Suratul Fat’hi Ta Tattare (II)

by Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani
4 days ago
0

Allah ya ce wa Manzon Allah (SAW) “Mu muka aiko...

kebance

Kebance-kebancen Manzon Allah (SAW) II

by Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani
3 weeks ago
0

Daga Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani, Masu karatu assalamu alaikum...

Kebance-kebancen Manzon Allah

Kebance-kebancen Manzon Allah (SAW) I

by Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani
4 weeks ago
0

A uzu billahi minas shaidanin rajim. Bismillahir rahmanir Rahim. Wa...

Next Post
Matsalar Bushewar Gaba Da Maganinta

Matsalar Bushewar Gaba Da Maganinta

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version