Tare da Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani,
Bismillahir rahmanir Rahim. Assalamu alaikum masu karatu.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata, muna bayani ne a kan gaibuka guda biyar da Allah ya sanar da Annabi (SAW), ba ma kawai sanin abubuwan da mutane suka boye a gidaddajinsu ko abincin da suke ba, irin na Annabi Isah (AS).
Kamar yadda muka yi bayani a makon jiya, Allah shi ya san yaushe ruwan sama yake sauka kuma ya sanar da Manzon Allah. Yanzu ma a wannan zamanin ga technology nan ya zo; sai ka ga kafura mai shiga ta rashin kamala ma tana fadar wannan ilimin da wuraren da za a yi ruwa a duniya. Yanzu ya kenan? Mai musu dai ba zai karyata Allah ba da ya ce shi kadai ya san saukar ruwan sama. Illa abin da zai iya cewa shi ne, Allah ne ya kawo wani abu na kimiyya ya sanar da kafuran nan ilimin abin. To, ko haka a gaya wa Annabi (SAW) a ce Allah ne ya sanar da shi mana, amma ba musu ba. Manzon yakan yi addu’a ba hadari kuma a saukar da ruwan sama. Ya taba cewa, Mala’ikan Ruwa ya fada masa zai je ya yi ruwa a Yemen.
Ba wata rai da ta san me Allah zai yi gobe. Ko da mutum ya tsara wa kansa ya rubuta cewa zai yi kaza da kaza gobe; ba dole ne abin ya tabbata ba. To shi ma kuma Allah yana sanar da wasu mutane hakan. Manzon Allah (SAW) ya ce ku ji tsoron hangen nesan mumini, domin shi yana gani ne da hasken Allah. Shi ya sa wani bawan Allah da ya kalle ka zai iya ba ka labarin rayuwarka gabadaya. To shi ma Manzon Allah a gaya masa ko haka mana, a ce Allah ne ya sanar da shi.
Babu ran da ta san a ina za ta mutu. Ba wani da zai iya cewa ga inda zai mutu sai wanda Allah ya sanar da shi. Akwai wani malami yana ba da labari, ya ce babansu yakan ce ba ku isa ku ga yadda za a binne ni ba, to zamanin tafiya Makka ne a kafa, shikenan sai kuwa ya tafi Makka a can ya rasu, sai dai kayansa aka dawo da su gida. Ko su wadanda suka dawo da kayan nasa gida, sun dai ga lokacin da aka yi masa sallah a harami amma tun da aka shigar da shi wurin da ake shiga babu wanda ya san yadda aka binne shi. To kun ga shi a nan Allah ya sanar da shi. To Manzon Allah (SAW) ya sanar da mutanen Madina cewa zai rayu a cikinsu kuma zai rasu a cikinsu. Kuma Manzon Allah ya ce “tsakanin mumbarina da kabarina dausayi ne na Aljanna” ka ga har ya san ga inda kabarinsa yake (SAW). Duk wannan ba karfi ya yi wa Allah ya sani ba, Allah ne ya sanar da shi, to meye abin rikici a ciki? Allah shi ne masani kuma shi yake sanar da abu. Kuma ya ba Manzon Allah (SAW) sanin wadannan gaibu biyar da ake fada.
Kuma Manzon Allah an ba shi sanin Ruhi. Rai yana daga cikin lamarin Ubangiji. Rai wani sirri ne, ma’ana rai wani abin halitta ne wanda ido ba ya iya gani amma kuma idan Allah ya bayar da idon gani sai a rika ganinsa. Fakarur Razi da Manawi (a cikin Sharhin Jami’us Sagiri) da Alusi (a cikin Ruhil Ma’ani) dukkansu sun tafi a kan cewa Allah Tabaraka wa Ta’ala ya ba Manzon Allah (SAW) dukkan wadannan gaibuka guda biyar kuma Allah ya ba shi iko ya yi hukunci da zahiri da kuma badini.
To, Annabi Isah (AS) an daga shi zuwa sama. Annabi (SAW) ya ce ya gan shi a sama ta biyu shi da Annabi Yahya (AS). To amma shi Manzon Allah ba sama ba, an kai shi Sidratul Muntaha, ya shige Mustawa, har sai da aka kai Kaba Kausaini Au Adna (SAW). To ka ga ya fi saman da aka kai Annabi Isah (AS). Kuma Annabi (SAW) a ranar tashin kiyama Allah zai ba shi ceto babba. Mumbarin da za a sa masa ranar kiyama babu wanda yake da irinsa (SAW).
Annabi Isah (AS) da Bani Isra’ila suka nemi kashe shi; Allah ya dauke shi, sai ya jefa wa wanda ya fi zakalkalewa irin jikin Annabi Isah, mutumin ya waiwayo da sifa irin ta Annabi Isah sai suka kashe shi. Shi kuwa Manzon Allah (SAW) lokacin da kafiran Makka suka nemi kashe shi, ya fito da ransa da jikinsa ya shige ta gabansu Allah ya makantar da su ba su gan shi ba.
To duk wadannan suna daga cikin abubuwan da Allah ya ba Annabawa kuma ya ba Annabi (SAW) har ma nashi ya fi nasu.