Daga Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani
Annabi Isma’il (AS) shi Allah ya ba wa Zamzam. Wanan ruwan zamzam da muke sha, asalainsa ya faro ne a lokacin da Annabi Isma’il yana yaro, bayan ruwa da dabinon da Annabi Ibrahim ya tanadar musu shi da Babansa a wurin da ya kai su ajiye; sun kare, Babarsa ta yi ta kai-komo, ta hau dutsen Safa da gudu ta sauko; ta hau dutsen Marwa da gudu ta sauko, har sai da ta yi wannan Safa da Marwan da muke yi. Har gobe idan muna Safa da Marwa, muna tuna kai-komon da Babar Annabi Isama’il (AS) ta yi ne kuma muna yin koyi. Har yau Makka gabadaya tuna wasu abubuwa na Annabawa ake ta yi. Babar ta yi ta hawa da saukan duwatsun har sai da ta yi sau bakwai, shi kuma Annabi Isma’il yana turje-turjen kafa a kasa (irin yadda yara jarirai ke yi idan suna kukan neman nono), wurin da yake turjawan nan Allah ya fito da ruwan zamzam ( a wata ruwaya). Ko kuma Mala’ika Jibrilu (AS) ne ya cakki wurin da fukafukinsa sai ruwan Zamzam ya fito, ruwa yana kara yana fitowa, Babar ta zo ta ga haka; ta sha ruwan ta shayar da danta sai ta ji koshi. Ruwa ne amma kuma abinci, to sai ta ce ma ruwan da harshensu na Ibraniyanci “Zamzam”, ma’ana tsaya a nan, tsaya a nan (kar ka yi yawo). Manzon Allah (SAW) a Hadisi yana cewa, “Allah ya jikan Mahaifiyar Isma’ilu, ba don ta ce ruwan Zamzam ya tsaya ba da ya game duniya”.
Yana daga mu’ujizar ruwan Zamzam, duk wata fasaha ko kimiyya an gwada amfani da ita domin janyo shi zuwa wani waje daga Harami amma ruwan bai fita, a iya Harami nan ruwan ya tsaya. Wannan rijiya mai albarka, a bisa albarkar Annabi Isma’il (AS) har tashin duniya ba za ta kare ba. Za ka ga mahukuntan kasar suna cewa an auna rijiyar an gani, idan ma aka fi diba ruwan da yawa ya fi bubbugowa da yawa. Sabanin fanfunanmu na zamani (bohole) shi idan aka fi diba da yawa ya fi ja da baya. Da duniya za ta taru kaf, Zamzam zai ishe ta saboda Kudurar Allah.
Shikenan bayan ruwan ya bubbugo, Babar Annabi Isma’il ta nemi ya tsaya a wurin da yake, Larabawan Jurhun sai suka ga tsuntsaye suna shawagi a wurin, sun san cewa a wannan garin (kafin ya zama Makka) idan aka ga tsuntsu yana shawagi cikin biyu ne, imma ya ga mushe ko kuma ya ga ruwa a wuri. Suna zuwa don su duba su gani sai suka ga rijiyar da aka dan hake, ga kuma uwa da danta a gefe. Suka tambaye ta ya aka yi ta samu wannan ruwa? Ta nuna musu ruwanta ne, sai suka nema daga wurinta cewa za su zauna su rika ba ta nono ita kuma ta rika ba su ruwa, ta amince. Sai suka kakkafa Khaimominsu (runfuna), wannan ne ya zama garin Makka. Suka zauna tare da ita suna ba ta abinci ita kuma tana ba su ruwa, da haka sai Annabi Isma’il (AS) ya tashi a cikinsu. Daga nan ne aka samu Arabul Musta’araba (Larabawan da suka ji Larabci wadanda asalinsu ba Larabawa ba ne), domin Annabi Isma’il (AS) Ba’ibrane ne (Dan kabilar Ibrananci).
To, a ci gaba da tarihin wannan rijiya ta Zamzam, da tafiya ta yi tafiya, su Larabawan Jurhun sai wata kabila ta zo ta yake su, ta kore su daga Makka. Lokacin da Larabawan Jurhun suka ji an ce ga wannan yakin ya taho musu, ba yadda za su yi su yake su wadannan abokan gaba, sai suka cike rijiyar da duwatsu, duk wani abu na Annabi Isma’il (AS) suka zuba a rijiyar, sannan suka shafe ta, wurin ya zama kamar Allah bai taba yin rijiya a wurin ba. Waccan kabila ta zo ta kama Makka, su ba su ma san da zancen rijiya ba har shekaru dubunnai, har sai da Allah ya kawo Abdulmuddalibi (Kakan Manzon Allah SAW). Allah ya nuna masa a mafarki cewa ya tashi ya haka “Barratu”, ya yi tunanin shin mene ne Barratu kuma? Tashi ka haka Zamzam, nan ma ya yi tunani mene ne Zamzam kuma? Nan dai ya fada wa Kuraishawa abin da ya gani a mafarki. Kuma ya ce ya yi tambaya mene ne Barratu an ce masa Zamzam. Kowa ya bushe da dariya, suna ganin batun tsufa ne ya sa shi haka. To kuma da aka samu masu tarihi sai suka ce eh, lallai an ce Kakansu Isma’ilu yana da rijiya, amma ba a san a ina rijiyar take ba.
Abdulmuddalibi ya kuma komawa barci, mai zuwa ya sake zuwa masa ya ce, tashi ka haka Barratu, tashi ka haka Zamzam. Ya tambaya, wai a ina abin yake, aka ce masa ka fito Kwarin Harami gobe, duk inda ka ga Hankaka ya zo yana tsattsagen ainci, nan ne wurin rijiyar; sai ka haka. Shikenan Dattijo ya zo da abin hakawa ya jira, can kuwa sai ga Hankaka ya zo yana tsattsagen abinci, daga nan ya zo ya kama hakawa, wasu na yi masa dariya. Shi ne har ya yi wannan bakance na cewa idan Allah ya hore masa haihuwar ‘ya’ya goma (10) zai yanka daya. Yana cikin aikin haken rijiyar sai suka fara ganin alamar shatin rijiya, masu masa dariya suka ce wai ko dai abin nan da gaske ne. Ya ci gaba da hakawa kuma sai ga zinare, nan masu masa dariyar suka ce wannan fa gadon kakansu ne; duk su za su raba a tsakaninsu. Nan dai har aka riska ruwa ya fito, masu masa dariya suka ce “ai wannan mun ji labarinta daga kakanninmu, rijiyar ta Makka ce bakidaya”. Abdulmuddalibi ya ce, “a’a, ni ne Allah ya bai wa”. Suka ce a koma wurin Bokar Yaman a tambaye ta, to suna tafiya a daji ruwa ya kare musu har suka ce su zauna su jira mutuwa kawai. Abdulmuddalibi ya ce “mu kuwa ma zauna mu jira mutuwa? A maimakon haka ai mu yi ta ci gaba da tafiya, duk wanda mutuwar ta zo masa shiekanan, kila a cikinmu wani zai kai”. Ya tashi ya hau rakuminsa ya bige shi, rakumi yana tashi daidai wurin sai ga ruwa. Masu gardama da shi suka ce a koma Makka kawai magana ta kare, Allah da ya ba shi (Abdulmuddalibi) ruwa a nan, shi ne ya ba shi wancan rijiyar. Don haka shayar da mutane ruwan rijiyar ta zama gadon ‘ya’yansa, har ma lokacin da Annabi (SAW) ya yi hijira, Amminsa Abbas shi ya ci gaba da shayar da ruwan rijiyar.
To ka ga shi ma Manzon Allah (SAW) Kakansa Abdulmuddalibi Allah ya sa ya sake haka rijiyar Zamzam da Annabi Isma’ilu ya haka. Rijiyar Zamzam mu’ujizar Annabi Isma’il ce amma ita ma Allah ya ba Manzon Allah (SAW) ita.